Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Dawo Daga Taron Kungiyar Tarayyar Afrika

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara na kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 6.

A ziyarar ta kwanaki biyu da ya kai kasar Ghana, shugaba Tinubu ya halarci taron a matsayinsa na shugaban hukumar gudanarwar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.

A cikin jawabinsa, shugaba Tinubu ya yi cikakken bayani game da ci gaban da ECOWAS ta samu a fannoni daban-daban da suka hada da yaki da ta’addanci, hada-hadar tattalin arziki, ayyukan jin kai, ilimi, kiwon lafiya, makamashi, ma’adanai, da noma.

Ya kuma jaddada cewa, an samar da rundunar tsaro ta ko-ta-kwana don yaki da ta’addanci, da inganta harkokin zabe da gudanar da harkokin mulki a tsakanin kasashe mambobin kungiyar,da yin hada hadar kasuwanci marar shinge a tsakanin mambobin kungiyar  da sauransu.

Bugu da kari, ya yi nuni da ayyukan jin kai na ECOWAS, kamar Dala miliyan 9 da aka ware domin tallafa wa wadanda abin ya shafa da kuma taimakawa kasashe mambobin a kokarinsu na yaki da ta’addanci.

Duk da wadannan nasarorin, shugaba Tinubu ya bayyana kalubalen da kungiyar ke fuskanta, da suka hada da hamayyar siyasa, ta’addanci, karancin abinci, sauyin yanayi, da kuma bata gari.

Ya kuma jaddada aniyar ECOWAS na wanzar da hadin kai, tattaunawa da kasashe mambobin kungiyar, da kuma gudanar da wani babban taro na musamman domin tattauna makomar al’umma.

 

Daga Bello Wakili

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara