Connect with us

Labarai

Shin komawar Cristiano Ronaldo Al-Nassr Ta Yi Amfani?

Published

on

A ranar 30 ga watan Disamban 2022 ce kyaftin ɗin tawagar ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya koma taka leda a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya.

Ya koma ƙungiyar ne a kan farashim Fam miliyan 200 duk shekara, wanda shi ne albashi mafi tsoka a ƙwallon ƙafa.

Sai dai tun bayan komawarsa Saudiya da taka leda, masu sharhi a kan harkar suke cigaba da tattauna nasarar da ya samu da akasin haka.

A ranar Asabar ce 17 ga Agusta ce Al-Hilal ta lallasa Al-Nassr da ci huɗu da 1 a wasan Saudi Super Cup.

Ronaldo ne ya fara zuwa ƙwallo a wasan bayan minti 44, inda magoya bayan ƙungiyar suka fara murna, kafin daga bisa murnar ta koma ciki.

Wannan na zuwa ne bayan a ranar 1 ga Yuni, Al-Hilal ɗin ta doke Al-Nassr a wasan Kofin Kings Cup, inda Al-Hilal ta yi nasara a bugun fanareti bayan an tashi canjaras.

Bayan an tashi wasan ne fitaccen ɗan wasan ya fashe da kuka, inda abokan wasansa suka taru a kansa suna ba shi haƙuri.

Haka kuma na biyu Al-Nassr ta ƙare a Gasar Sausi Pro League a kakar bara.

Har yanzu kofin da ya ci tun zuwansa ƙungiyar ita ce Kofin Arab Club ta kakar bara.

Ganin yadda Al-Hilal ke cigaba da kaka-gida a wasan ƙwallon Saudiyyar ce ya sa ake ganin shin akwai amfanin da zuwan Ronaldo ya yi wa Al-Nassr?

A ɓangaren zura kwallaye ba a cewa komai, domin a kakar bara ya kafa tarihin cin ƙwallaye a gasar, inda ya zura ƙwallo 35 a kaka ɗaya, inda ya karya tarihin Abderrazak Hamdallah, wanda ya taɓa zura ƙwallo 34 a kakar 2028-2019.

Zuwa yanzu, ɗan wasan na zura ƙwallo 67, ya taimaka an ci ƙwallo 16 a wasa 73 da ya buga wa ƙungiyar ta Al-Nassr.

Ke nan za a iya cewa a matakinsa da ɗan wasa, ya ci ƙwallaye, kuma ya nuna bajinta.

Duk kulob ɗin da ya buga wa ƙwallo ya lashe kofi, ciki har da Sporting CP, inda ya faro.

Sai dai yadda Al-Nassr ɗin ba ta lashe kofuna sosai, sai wasu ke ɗiga alamar tambaya a kan nasarar da ya samu a kolub ɗin.

Kafin komawarsa Al-Nassr, Ronaldo ya lashe kofuna da dama a ƙungiyoyin da taka leda, kamar Manchester United, da Real Madrid, inda ya fi lashe kofuna. Sannan ya lashe kofuna a ƙungiyar Juventus, inda ta je kafin ya koma Saudiyya.

Haka kuma ya lashe kambun Ballon dO’r sau biyar da sauran abubuwa da dama.

Ɗalhatu Musa Liman, ɗan jarida ne mai sharhi a kan wasanni da sauran al’amura, ya bayyana wa BBC cewa zuwan Ronaldo Gasar Saudi Pro League ya wuce maganar lashe kofi.

“Ai ana maganar ɗaga darajar ƙwallon ƙafar ƙasar ce baki ɗaya. Zuwansa gasar ƙasar ce baki ɗayanta ta ƙara armashi a idon duniyar baki ɗaya daga shekara 2 da suka gabata.”

Ya ƙara da cewa ita kanta Al-Nassr ɗin ta samu ƙarin magoya baya a duniya da ma kafafen sadarwa a sanadiyar zuwansa.

“Haka kuma zuwansa ɗin zai taimaka wajen samun damar ɗaukar nauyin Gasar Cin Kofin Duniya da Saudi Arabia ke hanƙoro. Don haka ya ci nasarar zuwa ƙasar da taka leda.

“Haka kuma za a iya iya cewa ya zama carbi ɗaya da ya tsinke, inda bayan zuwansa daga fitattun ƴan wasa daga Turai suka fara tafiya ƙasar da taka leda.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Fasaha48 mins ago

MDD Ta Yi Alla-Wadai Da Harin Isra’ila Kan Wata Makaranta A Gaza

Hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (Unrwa), ta yi Alla-wadai da harin da Isra’ila ta...

Labarai1 hour ago

‘Sakamakon Da Ghana Ke Samu Abin Kunya Ne A Wurinmu’

Ghana na daf da rasa damar halartar gasar nahiyar Afrika karon farko tun shekarar 2004, kuma yanzu haka ana ta...

Fasaha1 hour ago

Gwamnatin Kano Za Ta Hada Hannu Da Tsofaffin Dalibai Domin Inganta Ilimi

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta bayyana shirinta na hada kai da Tsofaffin Kungiyoyin dalibai a fadin Jihar domin inganta...

Kasuwanci1 hour ago

Jihar Neja Ta Kafa Hukumar Kayyade Farashin Kayyakin Masarufi

Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya amince da kafa hukumar kula da farashin kayyaki ta jihar Neja.  ...

Labarai1 hour ago

Tawagar Gwamnatin Tarayya Tayi Jaje Ga Al’ummar Jigawa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da tawaga domin jajantawa iyalan wadanda suka rasu a Majia, karamar hukumar Taura...

Kasuwanci2 hours ago

Dattawan Jam’iyar PDP Na Fadi Tashin Hade Kan ‘Ya’yan Jam’iyar – Abba Moro

Majalisar dattawan jam’iyyar PDP ta yi kira ga kungiyoyi masu fada a ji a jam’iyyar da su rungumi zaman lafiya...

Kasuwanci2 hours ago

Kano Ta Bada Miliyan 100 Ga Wadanda Fashewar Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin naira miliyan dari ga wadanda fashewar tanka ta shafa a garin Majia da...

Ilimi2 hours ago

Babu Aljannu Ko Rauhanai A Batun Ciwon Kwakwalwa – Dr. Poul

Wani likitan dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke lafiya, jihar Nasarawa Dr. Paul Agboand ya ce...

Kasuwanci2 hours ago

An Ƙaddamar Da Kwamitoci 6 Don Ƙara Inganta Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kafa ƙa’idojin gudanar da nagartattun ayyukan gwamnati a cikin ma’aikatun...

Fasaha2 hours ago

Dalibai Sun Babbake Gidan Shugaban Kwalejin Kimiyya A Birnin Kebbi

Daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Jega da ke jihar Kebbi sun kona gida da motar Shugaban kwalejin kimiyya da...

Mafi Shahara