Connect with us

Kasuwanci

Nijeriya Da UAE Sun Cimma Matsayar Ci Gaba Da Zirga-Zirgar Jiragen Sama Tsakanin Su

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da hukumomin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin ci gaba da zirga-zirga tsakanin ƙasashen biyu.

Hakan na nufin cewa ƴan Najeriya za su iya ci gaba da zirga-zirga zuwa birnin Dubai na ƙasar ta UAE.

A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce “bayan nasarar da aka samu wajen tattaunawa an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wadda za ta bai wa masu riƙe da takardar tafiya ta fasfon Najeriya samun izinin yin tafiya zuwa Haɗaɗɗiyar Daular ta Larabawa”.

Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga yau 15 ga watan Yulin 2024.

Wannan na zuwa ne sama da shekara biyu bayan da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da takardar biza ga ƴan Najeriya sanadiyyar ruɗani na diflomasiyya.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa na daga cikin ƙasashen da al’ummar Najeriya ke yawan ziyarta, ko dai domin kasuwanci ko kuma shaƙatawa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara