Connect with us

Labarai

Matashi Mai Yi Wa Kasa Hidima Ya Bada Tallafi A Asibitocin Jihar Zamfara

Published

on

A wani yunkuri na bunkasa kiwon lafiyar mata masu juna biyu a jihar Zamfara, wani matashi mai yi wa kasa hidima mai suna  Nwogu Chinonso, ya bayar da tallafin magunguna da sauran kayayyakin masarufi na daruruwan naira ga wasu cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da ke Gusau babban birnin jihar.

Da yake jawabi yayin kaddamar da kayayyakin a fadar mai martaba sarkin Gusau, jami’in hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC a jihar Zamfara, Alhaji Alhassan Abdulsalam ya yabawa matashin bisa wannan karamci.

Jami’in wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan sa ido kan ayyukan hukumar, Mista Isaac Maikur ya bayyana cewa, an kafa hukumar NYSC ne domin samar da hadin kai, zaman lafiya da cigaban kasa.

Ya jaddada cewa, aikin taimakawa al’umma wato CDS, shi ne ginshikin shirin na NYSC, tallafa wa marasa galihu.

Don haka Alhaji Alhasan ya gode wa Masarautar da wadanda suka dauki nauyin shirin bisa goyon bayan da suka bayar wajen ganin an cimma burin matashin na tallafawa rayuwar al’umma.

Da yake jawabi tun da farko, matashin,  Mista Nwogu Chinonso wanda ya iya gano bukatun al’ummar yankin da aka tura shi, tare da kawo wadanda suka tallafa wa shirin, ya yi kira ga masu hannu da shuni, kamfanoni, jihohi da ƙananan hukumomi da su ɗauki nauyin ayyukan taimakon al’umma na matasa masu yi wa kasa hidima.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, ya yabawa matashin bisa wannan karamcin, wanda ya ce, ya zo akan gaba, kuma zai taimaka matuka wajen rage kalubalen da mata ke fuskanta a lokacin haihuwa da ma bayan haihuwa.

Sarkin wanda ya samu wakilcin babban hakimin yankin, Alhaji Bashir Kabir Danbaba ya kuma yi kira ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke  jihar da su yi koyi da wannan matashi.

Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen ba da shawara ga matasan  da su zauna lafiya a duk inda suka tsinci kansu.

 

Daga Sani Dutsinma

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara