Connect with us

Kasuwanci

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Gargadi Kananan Hukumomi Game Da Tara Kudaden Shiga

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci mahukuntan kananan hukumomin jihar 44 da su kara himma wajen samar da kudaden shiga, inda ta yi gargadin cewa za su iya fuskantar rage kasafin kudin shekara mai zuwa idan suka kasa yin hakan.

 

Hakan ya biyo bayan tattaunawa ne a wani rahoto da aka gabatar kan asusun gwamnati da aka tantance dangane da kananan hukumomi 44 na wannan shekara ta 2018 da dan majalisa mai wakiltar mazabar Fagge Tukur Muhammad ya gabatar a zaman majalisar, wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta.

 

Mamba mai wakiltar Ungoggo Aminu Saa’du ya nuna damuwarsa kan yadda ake tafiyar da harkokin kudaden gwamnati. “ba tare da kwatankwacin komowa ba baya ga yawan dogaro da kason da gwamnatin tarayya ta ke bayarwa”

 

Ya bayyana cewa, kasancewar kasafin kudin shekara na sama da biliyan 60 daga kananan hukumomin da ke da kasa da rabin kudaden shiga, akwai bukatar majalisar ta samar da ingantaccen tsarin da zai sa su tashi zuwa akalla kashi 40-60 a duk shekara.

 

Ya yi nuni da cewa akwai dimbin albarkatun kasa da za a yi amfani da su da kuma samar da kudaden shiga amma sun kasa yin amfani da su.

 

“Saboda haka gidan ya kamata ya kafa doka mai tsauri da kuma bin hanyoyin da za su tsaya tsayin daka don cimma nasaara”

 

A karo na biyu dan majalisar mai wakiltar Rimin Gado Muhammad Bello Butu Butu ya jaddada bukatar kwamitin kasafin ya duba yadda kasafin kudin ke gudana.

 

KHADIJAH ALIYU/Wababe

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara