Connect with us

Kasuwanci

Joe Biden Ya Hakura Da Takarar Shugaban Amurka

Published

on

Shugaban Amurka Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin Amurka a wa’adin mulki na biyu.

Cikin jawabin da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban ya ce ya yi hakan ne domin ”masalahar jam’iyyarsa da kuma ƙasarsa”.

Ya ce cikin shekara uku da rabi da ya yi yana jagorantar Amurka, ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

”A yau Amurka na da ƙarfin tattalin arziki a duniya, mun kafa tarihi a fannin zuba jari domin sake gina ƙasarmu”.

”A lokacin da muka ɗauka muna mulki mun samar da muhimman abubuwa ciki har da dokar mallakr bindiga”.

Shugaban ya kuma goyi bayan mataimakiyar Kamala Haris a matsayin wadda za ta yi takarar shugabancin ƙasar a madadinsa.

”A yau ina son in jaddada cikakken goyon bayana ga Kamala a matsayin ‘yar takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyarmu, lokaci ya yi da za mu haɗa kai wuri guda domin kayar da Donald Trump”, kamar ya wallafa a shafinsa na X.

A baya-bayan nan dai shugaban ya fuskanci matsin lamba daga manyan ‘yan jam’iyyarsa da ke kiraye-kirayen ya haƙura da takara, tun bayan rashin katabus a muhawarsa da Donald Trump

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara