Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Samar Da Kananan Jiragen Ruwa A Kananan Hukumomi 3

Published

on

A kokarinta na dakile afkuwar hadurran kwale-kwale da ake yawan samu tare da asarar rayuka da dama, gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na samar da sabbin jiragen ruwa ga kananan hukumomi uku da wannan lamari ya fi shafa.

Kwamishinan Sufuri na jihar  Injiniya Muhammad Diggol ya bayyana haka a wata ziyarar da ya kai kananan hukumomin Bagwai, Garko, da Tudun Wada.

Injiniya Muhammad Diggol ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na kokarin da Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ke yi na inganta harkar sufuri da kuma bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin al’umma a wadannan yankuna.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin mai ba da shawara na musamman kan harkokin sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sanya wannan kudiri a cikin kasafin kudin bana domin samun nasarar shirin.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar Ibrahim Adamu Kofar Nassarawa ya rabawa manema labarai, tawagar ta ziyarci Badau da ke  Bagwai, da Kafin Ciri da ke Garko, da kuma Maraku a karamar hukumar Tudun Wada.

Ya bukaci al’ummar da ke wadannan yankuna da su marawa gwamnati mai ci baya domin ciyar da yankunan gaba.

A nasu jawabin, shugabannin riko na kananan hukumomin Bagwai, Alhaji Aliyu Bello Gadanya, da na Garko, Malam Gambo Isa, da kuma na  Tudun Wada, Malam Umar Isa Rugu-Rugu, sun bayyana matukar farin cikinsu bisa wannan ziyarar.

Sun yi alkawarin kiyaye duk wata doka da gwamnatin jihar ta shimfida.

Sun tabbatar da bada cikakken goyon bayansu da haɗin kai don cimma manufofin da aka tsara.

 

Daga Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara