Connect with us

Labarai

Gwamnatin Borno Ta Gargadi Daliban Sakandare Game Wuce Gona Da Iri

Published

on

Gwamnatin jihar Borno ta gargadi masu makarantu masu zaman kansu da dukkan shugabannin sakandire da su ja kunnen daliban aji 6 da suka kammala rubuta jarabawarsu ta karshe game da aikata ayyukan da ba su dace ba da sunan taya juna murna.

Kwamishinan ilimi, kimiya, fasaha da kirkire-kirkire, Alhaji Lawan Wakilbe ya yi wannan gargadin a wajen wani taro da kungiyar shugabannin makarantun sakandire ANCOPSS, masu  makarantu masu zaman kansu, sakatarorin ilimi da sauran manyan jami’an ma’aikatar.

Ya nuna matukar damuwarsa kan irin munanan dabi’u da daliban makarantun sakandaren da suka kammala karatu ke yi, musamman a karshen jarabawarsu.

Kwamishinan ya yi karin haske kan wasu ayyukan da ake tafkawa da suka hada da lalata makarantu da kadarorin gwamnati da daliban ke yi, da rubuce-rubucen da ba su dace ba a kan tufafinsu, da shagulgulan da ba su dace ba a wurare daban daban a fadin jihar.

Ina muku gargadin cewa ddukan  makarantu  masu zaman kansu da aka samu sun saba wa wadannan ka’idoji, za su fuskanci mummunan hukunci, ciki har da yiwuwar rufe makarantun” Inji Wakilbe.

Sakataren Ilimi na Birnin Maiduguri Dakta Mala Kulloma, da wakilin shugabannin makarantun Sakandare Abba Ali Ladan, da na makarantu masu zaman kansu, Babagana Alkali, sun bayyana kudurinsu na ganin cewa babu wani dalibin da ya kammala karatunsa na karshe da ya shiga ayyukan rashin da’a.

Sun sanar da cewa duk dalibin da aka samu da aikata ba dai-dai ba, zai fuskanci mummunan hukunci, ciki har da hana shi sakamakonsa.

Hakazalika, Kwamishinan Ilimi, Lawan Wakilbe, ya bukaci goyon baya da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da bikin yaye daliban cikin lumana.

A ziyarar da ya kai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Mohammed Yusuf, kwamishinan ya yi kira da a ci gaba da sanya ido a dukkan makarantun gwamnati da na sakandire masu zaman kansu a tsawon wannan mako da ake shagulgulan kammalakaratu.

Kwamishinan ‘yan sandan wanda mataimakin kwamishina Mohammed Bello ya wakilta, ya tabbatar da cewa an samar da matakan da suka dace don hana tabarbarewar doka da oda.

Hakazalika kwamishinan ilimin ya  kai ziyara hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya wato NSCDC.

 

Daga Dauda Iliya

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara