Connect with us

Kasuwanci

Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Kashi Na 2 Na Tallafawa Mata A Jihar

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da wani shiri na tallafawa mata 5,200 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Da yake jawabi a wajen wani gagarumin biki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce  wadanda suka ci gajiyar shirin zasu karbi tallafin naira 50,000 kowanne su  domin  dogaro da kansu.

Ya ce matakin hakan na da nufin rage wahalhalun rayuwa da mutane ke fuskanta musamman mata, domin inganta tattalin arzikin a tsakanin al’umma.

Ya ce gwamnatinsa ta kudiri aniyar ware Naira miliyan 260 duk wata domin gudanar da shirin, wanda hakan na cikin kokarin gwamnatinsa na karfafa matasa da mata da kuma biyan basussukan fansho.

Ya bukace su da su yi amfani da gogewar da suka samu a lokacin horon da aka ba su kan yadda za su shiga kananan sana’o’i, da nufin cimma burin da aka sa gaba.

Gwamnan ya yi kira ga mata da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaftar muhalli musamman a wannan lokaci na damina, da nufin inganta harkokin kiwon lafiya.

A cewar Gwamna Yusuf, “An yi ayyuka da yawa a fannonin ilimi, kiwon lafiya, da koyar da sana’o’i”, yana mai jaddada cewa wannan shiri na nuni ne da yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a aiwatar da irin wannan karfafawa ga mazaje da nufin dogaro da kai da kuma daukar ma’aikata.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara