Connect with us

Labarai

Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar

Published

on

Biyo bayan rushewar masallacin garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar, Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya bayar da gudunmawar Dala dubu 10 domin sake gina masallacin.

Masallacin dai na da dadadden tarihi domin an gina shi ne tun  shekaru 200 da suka wuce.

Gwamna Radda ya bayar da gudunmawar ne ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, wanda ke rike da sarautar ‘Turakin Damagaram’.

Yayin da yake bayyana godiyarsa ga Gwamnan bisa gudunmawar, mai alfarma Sarkin Musulmin Damagaram, Sultan Umaru Sanda, yace tallafin zai taimaka matuka wajen sake gina masallacin.

Ya ce gudunmawar hakan za ta inganta dadaddiyar alakar da ke tsakanin jihar Katsina da masarautar Damagaram wadda ta kai shekaru 500.

A nasa jawabin, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ya shaida wa Sultan Umaru Sanda cewa Gwamna Dikko Radda ya bada gudunmawar ne saboda inganta tarbiyyar addini a masarautar.

Wannan masallacin zai taimaka wajen cusa tarbiyyar addinin Musulunci a cikin al’ummarmu, kuma hakan zai taimaka wajen magance matsaloli da dama a cikin al’umma.

Mu al’umma daya ce da turawa suka raba tsakaninmu, shi ya sa ya kamata mu karfafa alakar da ke tsakanin al’ummarmu kuma mu hada kai wajen magance kalubalen da muke fuskanta baki daya,” inji Gwajo-gwajo.

 

Daga Isma’il Adamu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Ilimi20 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha20 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai21 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai21 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai21 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi22 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha22 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci22 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai22 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara