Labarai
An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne
Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na uku na gidan bene a Buenos Aires, kamar yadda ‘yansanda suka bayyana.
Wata sanarwa ta ce ‘yansanda sun ga gawar Payne bayan da masu aiki ceto suka garzaya unguwar Palermo a ranar Laraba, bayan da suka samu rahoton faruwar wani abin tayar da hankali.
Payne mai shekaru 31, ya samu shahara ne sakamakon haɗa tawagarsu a shirin X Factor a shekara ta 2010 tare da Harry Styles, Louis Tomlinson, Niall Horan da Zayn Malik.
Tun da farko a wannan watan, Payne ya halarci kallon kuwa a Argentina tare da daya daga cikin ‘yan One Direction, Niall Horan.
Sa’o’i kafin mutuwarsa, Payne ya wallafa a shafinsa na Snapchat cewa: “Yau rana ce me daɗi a Argentina.”
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa
-
Labarai6 days ago
Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro
-
Labarai6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa
-
Labarai6 days ago
An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL
-
Labarai4 days ago
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram
-
Labarai6 days ago
Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar
-
Labarai4 days ago
Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa
-
Labarai4 days ago
Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar