Connect with us

Labarai

An Ciro Gawawwakin Baƙin Haure 89 Daga Teku

Published

on

Jami’an tsaron gaɓar tekun Mauritaniya sun tsamo gawawwakin baƙin haure 89 daga teku, wadanda kwale-kwale ya kife da su a ranar Litinin.

An ceto mutum tara da suka hada da yarinya ƴar shekara biyar, amma wasu da dama sun ɓata.

A cewar waɗanda suka tsira, kwale-kwalen da suke ciki ya taso ne daga yankin iyakar Senegal da Gambiya a makon jiya ɗauke da mutu 170.

Jirgin ruwan ya kife ne a gaɓar tekun kudu maso yammacin ƙasar ta Mauritaniya.

Kasar Mauritaniya dai ta kasance wata muhimmiyar hanya da bakin hauren da ke yunƙurin isa Turai daga yammacin Afirka ke amfani da ita.

Dubban kwale-kwale ne ke tashi daga kasar kowace shekara, inda tsibirin Canary, wani bangare na Sifaniya, ya kasance wurin da aka fi zuwa.

A bara, kusan baƙin haure 40,000 ne suka isa tsibirin Canary, a cewar gwamnatin Spain inda adadin ya nunka na shekarar da ta gabata.

Kungiyar agaji ta Caminando Fronteras ta yi ƙiyasin cewa sama da baƙin haure 5,000 ne suka mutu a yunƙurin shiga ƙasar Sifaniya ta teku a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2024.

A watan Afrilu, Tarayyar Turai ta bai wa Mauritania tallafin Yuro miliyan 210 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 225, inda aka ware kusan Yuro miliyan 60 don yaƙi da ƙauran ‘ƴan ci rani zuwa Turai ba tare da izini ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara