Connect with us

Labarai

Al’ummar Kauru Na Cikin Zullumi Bayan Lalacewar Gadar Da Ta Hadasu Da sauran Al’ummomin Jihar Kaduna

Published

on

Ambaliya ta lalata hanya da gada tare da barin matafiya cikin zullumin rashin sanin ina zasu nufa a Garin Kauru hedikwatan karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Al’ummar Garin na Kauru sun nuna damuwarsu kan mummunar ambaliyar ruwa da ta lalata wani bangare na hanya da gadar da ke hada garin Kauru, da sauran al’ummomi, inda yanzu haka matafiya suke can sun rasa nayi sabida wannan ce kadai hanyar da ake amfani da ita.

Wani shaidar gani da ido, Chiroman Yada Labaran Kauru Malam Sani Abanke, ya ce hanyar da abin ya shafa wanda ya hada Panbeguwa a karamar hukumar Kubau zuwa garin Kauru da kauyuka da dama da ke kewaye, hanya ce mai matukar muhimmanci wajen kwashe amfanin gonaki, sai gashi yanzu ruwa ya mata gyara.

Ya bayyana cewa barnar ta yi tasiri sosai ga tattalin arzikin yankin da kuma rayuwar yau da kullum, saboda mazauna yankin sun dogara sosai kan wannan titin don sufuri da kasuwanci.

Sauran masu amfani da hanyar da aka zanta da su sun yi kira da a yi gaggawar gyaran hanyar kafin ta gagari kunduli, tare da kira ga gwamnati a dukkan matakai su ja damara domin shawo kan lamarin.

Sun Kuma jaddada mahimmancin yin gyare-gyaren gaggawa don dawo da hanyoyin shiga da kuma tabbatar da tsaro da jin dadin jama’ar yankin.

Da yake jawabi a wurin da lamarin ya faru, bayan ziyarar gani da ido, Mai Martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakariyya Ya’u Usman, ya bayyana cewa akwai bukatar a dauki matakin gaggawa domin gyara halin da hanyar ke ciki.

A cewar Mai martaba yanayin hanyar ba kawai ya hana zirga-zirgar jama’a da kayayyaki ba, har ma yana haifar da babban hadari ga masu kokarin bin hanyar da ta lalace.

Don haka mai martaba Sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta ba da fifikon wajen aikin sake ginawa tare da samar da abubuwan da suka dace.

Ya kuma jaddada bukatar samar da mafita mai dorewa don hana afkuwar al’amura a nan gaba da kuma tabbatar da ci gaban al’umma a yankin.

Al’ummar Karamar Hukumar Kauru na fatan za a saurari kokensu kuma za a dauki matakin gaggawa don magance barnar da ambaliyar ruwan ta yi da kuma dawo da hanyar,

Alhaji Zakariyya Ya’u II ya ci gaba da cewa a yayin da damina ke ci gaba da kara kaimi, lamarin ya kara tabarbarewa, kuma mazauna yankin sun jajirce wajen yin kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo musu dauki domin rage musu radadin halin da suke ciki da kuma inganta ababen more rayuwa a karamar hukumar Kauru.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa kusan shekaru tara kenan da gwamnatin da ta gabata ta bayar da kwangilar sake gina wannan hanya mai matukar muhimmanci.

A halin da ake ciki, mazauna yankin na ci gaba da fuskantar ƙalubale masu yawa yayin da suke ƙoƙarin nemo madadin hanyoyin sufuri da samun damar yin ayyuka masu mahimmanci.

COV/YUSUF ZUBAIRU KAURU 

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara