Fasaha
Kamala Harris Ta Ce Tana Alfahari Da Goyon Bayan Da Take Samu
Mataimakiyar shugabar kasar Amurka Kamala Harris ta ce tana alfahari da samun dimbin goyon bayan da ake bukata domin zama ‘yartakarar jam’iyyar Democrat a zaben shugaban kasa.
Tana magana ne bayan binciken da aka gudanar ya gano cewa za ta samu yawan wakilan masu zaben da ake bukata wajen zabarta a matsayin ƴartakarar jam’iyyar Democrats, bayan da shugaba shugaba Joe Biden ya janye daga takara.
Zuwa yanzu, dukkan wadanda ake tunanin za su yi takara da ita sun mara mata baya, Tun da farko ta fara yakin neman zabenta a Delaware mahaifar shugaba Biden, inda ta shaidawa magoya bayanta cewa za ta tsallakar da Amurkawa tudun mun tsira daga abin da ta kira barazanar Trump
Ta yi alkawarin inganta rayuwar marasa karfi, da yaki da mallakar bindiga da kuma kare ‘yancin mata na zubar da ciki idan aka zabe ta.
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa
-
Labarai6 days ago
Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro
-
Labarai6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa
-
Labarai6 days ago
An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL
-
Labarai4 days ago
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram
-
Labarai6 days ago
Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar
-
Labarai4 days ago
Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa
-
Labarai4 days ago
Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar