Connect with us

Labarai

Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro

Published

on

 

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa kan Tsaro tare da jan hankalin mambobin da su yi aiki da kyawawan ka’idojin duniya wajen rage hadurran ababen hawa.

Ya kuma bukaci majalisar da ta ayyana manufofin Tsaron Hanyoyi na Kasa da tabbatar da ingantaccen hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi don cimma muradun tsaron hanyoyi tare.

Yayin da yake jawabi a lokacin bikin kaddamarwa a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya jaddada muhimmancin tsaron hanyoyi, yana mai cewa, “Tsaron hanyoyi ba kawai manufar gwamnati ba ce, amma wani muhimmin bangare ne na hanyar rayuwa da ke hada al’umma da juna a kasar nan.”

Ya kuma yaba da jajircewar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), yana mai cewa hukumar ta “girmama tare da tsarawa ingantacciyar dabarar magance kalubalen zirga-zirga a kasar nan” a cikin dan kankanin lokacin da ta kasance.

Kafuwar NaRSAC ta yi daidai da shawarwarin Rahoton Duba Karfin Kasa na Bankin Duniya, wanda ya gano wasu wuraren da ake bukatar gyara a cikin tsarin gudanar da hanyoyi da kuma tsaron hanyoyi a Najeriya.

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bukaci Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, da ya rungumi wadannan shawarwari a matsayin “wani ginshiki na gyare-gyaren da ake matukar bukata a wannan bangare.”

Haka kuma, Kashim Shettima ya yabawa yadda ake samun hadin kai tsakanin shugabannin gwamnatin tarayya da na jihohi, tare da wasu hukumomin gwamnati, yana cewa, “Wannan ruhin hadin kai ya bayyana mahimmancin aiki tare don amfanin kowa da kowa.”

Mataimakin Shugaban Kasar ya lura cewa wannan shirin ya yi daidai da alkawarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karfafa karfin gudanar da mulki a hukumomin gwamnati.

“Ina da tabbacin cewa wannan shirin zai inganta tsarin sufuri a Najeriya kuma zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa mai dorewa,” in ji Sanata Shettima.

A cikin jan hankalin da ya yi wa sabbin mambobin majalisar da aka kaddamar, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya jaddada rawar da za su taka na “ayyana manufofin Tsaron Hanyoyi na Kasa da tabbatar da hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi, da kananan hukumomi don cimma muradun tsaron hanyoyi tare.”

Tun da farko a jawabinsa, Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, Shehu Mohammed wanda kuma shi ne sakataren majalisar shawara, ya ce kaddamar da majalisar ya bude sabon babi a harkar gudanar da tsaron hanyoyi a Najeriya, wanda ya hada da saurin aiwatar da Manufar Tsaron Hanyoyi ta Najeriya (NRSS), wadda ita ce martanin kasar kan kira na amfani da hanyoyi cikin tsaro.

Ya ce kaddamar da majalisar ya nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa a kan hanyoyi, yana mai lura da cewa aiwatar da NRSS ya bayar da ingantaccen jagora na cimma burin tsaron hanyoyi, ta amfani da tsarin “ingantaccen tsarin tsaro” da duniya ta amince da shi don tafiyar da harkar tsaron hanyoyi.

Yayin da yake sake jaddada muhimmancin aiwatar da NRSS a matsayin babban abu na majalisar, Shugaban Hukumar ya ce yanzu Najeriya tana da damar rage yawan mace-mace zuwa sifili, wadanda ake samu daga hadurran ababen hawa.

NaRSAC na da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a matsayin shugaban, tare da mambobin da suka hada da gwamnoni guda shida, wanda kowanne ke wakiltar daya daga cikin shiyyoyin siyasa guda shida na kasar; Ministocin Sufuri, Ayyuka, Lafiya, Shari’a, Ilimi, Kudi, Muhalli, Harkokin ’Yan Sanda, Harkokin Cikin Gida, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, FCT, Labarai da Ayyuka da Kuma Yin Amfani da Albarkatun Jama’a.

Sauran mambobin sun hada da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa, Shugaban Kungiyar Kananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu ta Najeriya (NACCIMA), da Kungiyar Injiniyoyin Najeriya.

Bello Wakili.

Labarai

Ilimi20 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha20 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai21 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai21 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai22 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi22 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha22 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci22 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai22 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara