Labarai
Yaƙin M23 Ya ci Gaba a Congo Duk da Sulhu da Rwanda
Bayan da ƙasashen biyu maƙwabtan juna na Congo da Rwanda suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Donald Trump ya bayyana a matsayin mai cike da tarihi, jagoron na Amurka ya jinjinawa shugabannin ƙasashen biyu waɗanda ya ce sun yi hangen nesa wajen amincewa da kawo ƙarshen zubar da jinin dubban mutane tsawon shekaru.
An dai haska wannan zaman sanya hannu kai tsaye ta gidajen talabijin, inda shugabannin biyu wato Felix Tshisekedi na Jamhuriyyar Congo da Paul Kagame na Rwanda suka rattaɓa hannu a yarjejeniyar a gaban idon Donald Trump can a birnin Washington.
A cewar Trump shugabannin biyu sun ajje banbance-bambancen da ke tsakaninsu wajen rungumar zaman lafiya don jama’arsu.
Sai dai an sanya hannu a yarjejeniyar can a Washington dai dai lokacin da ake ganin ci gaban yaƙi tsakanin Sojin Congo da mayaƙan M23 da Rwanda ke marawa baya a kudancin lardin Kivu.
Babu dai wakilcin M23 a wannan tattaunawa ta Washington, hasalima basu aminta da yarjejeniyar da ka cimma a zaman ba, maimakon haka suna halartar nasu taron na daban wanda Qatar ke jagorantar sulhunta su da Congo a birnin Doha.
Masu sharhi na ganin abu ne mai matuƙar wahala, yarjejeniyar ta birnin Washington ta yi tasiri wajen kawo ƙarshen wannan yaƙi na shekaru.
Yarjejeniyar na zuwa a dai dai lokacin da Amurka ke son zuba jari a ɓangaren haƙar ma’adinai a Congo inda a gefe guda itama Qatar ke faɗaɗa shirinta na zuba jari a ƙasashen Afrika.
-
Ilimi7 days agoFarfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
-
Labarai3 days agoHukumar Raya Kogin Benuwe Ta Bullo da Sabuwar Fasahar Kare Hanyar Ban-ruwa a Tafkin Geriyo
-
Ilimi3 days agoAn Gudanar da Liyafar Taya Murna ga Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Dutse
-
Labarai5 days agoGwamnatin Tarayya ta Bada Tallafin Kayayyakin Aiki Gona ga Ƙananan Manoma a Jigawa
-
Labarai6 days agoAn Fara Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu na Bana
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita
-
Labarai6 days agoJigawa: Hukumar Alhazai ta Bai wa Amirul Hajji Tabbacin Cikakken Goyon Baya
