{"id":9998,"date":"2026-09-21T16:20:34","date_gmt":"2026-09-21T16:20:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9998"},"modified":"2026-09-21T16:20:34","modified_gmt":"2026-09-21T16:20:34","slug":"dakarun-soji-sun-ceto-mutane-23-tare-da-kama-lakurawa-hudu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/dakarun-soji-sun-ceto-mutane-23-tare-da-kama-lakurawa-hudu\/","title":{"rendered":"Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Nasir Malali\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Ha\u0257in Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane hu\u0257u da ake zargin mambobin \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta Lakurawa\u00a0 a Jihar Sakkwato.<\/p>\n<p>Jami\u2019in Ya\u0257a Labarai na Rundunar, Laftanar Janar Aliyu Danja, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce dakarun sun samu nasarori a wasu ayyuka daban-daban da suka gudanar a sassan jihar, da nufin dakile ayyukan \u2018yan ta\u2019adda.<\/p>\n<p>A ranar 20 ga watan Satumban 2026, dakarun sun kai dauki a harin da \u2018yan ta\u2019adda suka kai Sabon Gari a \u0198aramar Hukumar Wurno, inda suka yi musayar wuta da maharan tare da tilasta musu ja da baya. Dakarun sun kuma ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kai wani farar hula da ya samu raunin harbin bindiga asibiti.<\/p>\n<p>A wani samame, dakarun sun yi wa \u2018yan ta\u2019adda kwanton bauna a kusa da Chabe Biyu da ke \u0198aramar Hukumar Sabon Birni, bayan samun bayanan sirri kan yun\u0199urin da suke yi na ratsa hanyar Sabon Birni zuwa Takatsaba. Haka kuma, an ceto wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su bayan artabu da \u2018yan ta\u2019adda a hanyar Isa zuwa Kwanar Isa zuwa Shinkafi. \u018aaya daga cikin wa\u0257anda aka ceto ya samu karaya an kuma\u00a0 kai shi Babban Asibitin Isa.<\/p>\n<p>A \u0198aramar Hukumar Illela kuwa, dakarun sun kama mutane hu\u0257u da ake zargin mambobin Lakurawa ne, bayan samun bayanan sirri kan yadda suke tafiya da garken shanun da aka sace daga \u0199auyen Sarma zuwa Illela. An kuma kwato shanu shida a yayin samamen.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce nasarorin sun nuna tasirin ayyukan dakarun da ke amfani da bayanan sirri wajen dakile ayyukan ta\u2019addanci, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma hana \u2018yan ta\u2019adda damar zirga-zirga cikin sau\u0199i a yankin da ake gudanar da ayyukan ha\u0257in gwiwa.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir\u00a0<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Nasir Malali\u00a0 Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Ha\u0257in Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane hu\u0257u da ake zargin mambobin \u0199ungiyar ta\u2019addanci ta Lakurawa\u00a0 a Jihar Sakkwato. Jami\u2019in Ya\u0257a Labarai na Rundunar, Laftanar Janar Aliyu Danja, ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":0,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[522,2128,625,541],"class_list":["post-9998","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-ceto","tag-dakaru","tag-lakurawa","tag-sakkwato"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9998","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9998"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9998\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10002,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9998\/revisions\/10002"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9998"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9998"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9998"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}