{"id":9995,"date":"2026-09-21T13:49:48","date_gmt":"2026-09-21T13:49:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9995"},"modified":"2026-09-21T13:49:48","modified_gmt":"2026-09-21T13:49:48","slug":"nwdc-ta-sanya-tsaro-a-matsayin-babban-fifikon-ta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nwdc-ta-sanya-tsaro-a-matsayin-babban-fifikon-ta\/","title":{"rendered":"NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta"},"content":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu, Kaduna<\/p>\n<p>Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a cikin shirye-shiryen tallafa wa ci gaban yankin, tana mai cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne ginshi\u0199an samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ma\u2019ana.<\/p>\n<p>Babban Daraktan Gudanarwa na hukumar, Farfesa Abdullahi Shehu Ma\u2019aji, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyin jama\u2019a kai tsaye ta wayar tarho a cikin shirin Sashen Hausa Radio Nijeriya Kaduna Hannu Da Yawa na tsawon sa\u2019o\u2019i biyu.<\/p>\n<p>Farfesa Ma\u2019aji ya ce shirye-shiryen tallafa wa ci gaban yankin na hukumar za su shafi muhimman fannoni da suka ha\u0257a da ilimi da kiwon lafiya da noma da kare muhalli da samar da ayyukan yi, da kuma \u0199arfafa gwiwar matasa da mata.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa rashin tsaro na haifar da mummunan tasiri ga ci gaba ta fannoni daban-daban, musamman ta hanyar hana manoma zuwa gonakinsu da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da shafar halartar \u0257alibai a makarantu, da kuma takaita damar zuba jari.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cTaimakawa wajen dawo da tsaro a yankin Arewa Maso Yamma shi ne babban fifikonmu a cikin shirye-shiryen tallafa wa ci gaba. Ba za mu iya samun ci gaba a fannin ilimi da noma ko masana\u2019antu ba, matu\u0199ar al\u2019ummarmu ba za su iya zuwa gonakinsu ko su kwanta barci cikin kwanciyar hankali ba.\u201d<\/p>\n<p>Dangane da fannin ilimi, shugaban hukumar NWDC ya sanar da cewa za a gudanar da gagarumin aikin inganta gine-ginen makarantu a fa\u0257in jihohi bakwai na yankin, ciki har da gyaran gine-ginen makarantu da suka lalace da samar da kayan koyarwa na zamani.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201c\u2019Ya\u2019yanmu na karatu a \u0199ar\u0199ashin bishiyoyi da kuma gine-ginen da suka lalace. Hukumar za ta gyara makarantu tare da samar da kayan koyarwa na zamani, domin bai wa yaranmu ingantaccen ilimin da ya dace da su.\u201d<\/p>\n<p>A wani mataki na bun\u0199asa harkokin tattalin arziki da samar da ayyukan yi, Farfesa Ma\u2019aji ya bayyana shirin kafa banki a matsayin wani aikin hukumar, tare da \u0199o\u0199arin farfa\u0257o da masana\u2019antun da suka daina aiki a fa\u0257in yankin.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cMuna shirin kafa wani banki da hukumar za ta mallaka a matsayin wani reshe nata. Haka kuma, za mu farfa\u0257o da sauran kamfanonin da suka daina aiki a yankin. Wannan zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin yankin tare da samar da dubban ayyukan yi ga \u0257imbin matasanmu.\u201d<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa hukumar na tattaunawa da masu zuba jari daga cikin Najeriya da wajen \u0199asar, domin bun\u0199asa damar noma da Kuma dinbin al&#8217;ummar da ake dasu don samar ku\u0257i da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cMuna gayyatar masu zuba jari daga cikin \u0199asa da wajen \u0199asa. Yankin Arewa Maso Yamma yana da albarkar filayen noma masu fa\u0257i da kuma \u0199wararrun ma\u2019aikata. Muna son mayar da wannan dama zuwa arziki.\u201d<\/p>\n<p>Babban jami\u2019in hukumar ya yi kira da a \u0199ara ha\u0257in gwiwa tsakanin hukumar da gwamnatocin jihohi da sarakunan gargajiya da shugabannin \u2018yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, domin cimma manufofin ci gaban hukumar.<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cMuna bu\u0199atar goyon bayan gwamnoninmu da sarakunanmu na gargajiya da kuma dukkan attajirai maza da mata \u2018yan asalin Arewa Maso Yamma.<\/p>\n<p>Sarakunan gargajiya da attajirai da masu ilimi suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da nasarar wannan hukuma.\u201d<\/p>\n<p>Farfesa Ma\u2019aji ya yaba wa Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu bisa kafa hukumar, yana mai bayyana hakan a matsayin wani mataki da ya zo a kan lokaci domin magance matsalolin ci gaban da suka da\u0257e suna addabar yankin.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa: \u201cDole ne mu yaba wa Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesansa na kafa wannan hukuma. Yanzu muna bu\u0199atar addu\u2019o\u2019in kowa da kowa domin tabbatar da nasararmu.\u201d<\/p>\n<p>Masu kiran waya da suka bada tasu gudummuwa a shirin sun bu\u0199aci shugabannin hukumar da su sauke nauyin da ke kansu cikin gaskiya da ri\u0199on amana da tsoron Allah.<\/p>\n<p>Haka kuma, sun yi kira da a ci gaba da mai da hankali kan matsalar rashin tsaro da \u0199alubalen da ake fuskanta a fannonin kiwon lafiya da ilimi, da kuma rashin aikin yi da ke addabar al\u2019ummomi a fa\u0257in yankin Arewa Maso Yamma.<\/p>\n<p>Mohammed Aminu Abdullahi (Gombi) da Umar S. Fada ne suka jagoranci shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan kammala shirin, Mukaddashin Daraktan Shiyya ya zagaya da Farfesa Ma\u2019aji a harabar gidan rediyon Najeriya Kaduna, inda suka duba wasu wurare da aka gano suna bu\u0199atar \u0257aukar matakan gaggawa na gyara. Daga nan ne suka wuce zuwa wani taron sirri.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a cikin shirye-shiryen tallafa wa ci gaban yankin, tana mai cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne ginshi\u0199an samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa mai ma\u2019ana. Babban Daraktan Gudanarwa na hukumar, Farfesa Abdullahi Shehu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":0,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[],"class_list":["post-9995","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-labarai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9995","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9995"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9995\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9997,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9995\/revisions\/9997"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9995"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9995"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9995"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}