{"id":9962,"date":"2026-09-15T09:12:30","date_gmt":"2026-09-15T09:12:30","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9962"},"modified":"2026-09-15T09:12:30","modified_gmt":"2026-09-15T09:12:30","slug":"unicef-ta-%c6%99addamar-da-shirin-koyar-da-yan-mata-sanaoi-a-katsina","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/unicef-ta-%c6%99addamar-da-shirin-koyar-da-yan-mata-sanaoi-a-katsina\/","title":{"rendered":"UNICEF Ta \u0198addamar Da Shirin Koyar Da \u2019Yan Mata Sana\u2019o\u2019i A Katsina"},"content":{"rendered":"<h3>Daga Isma&#8217;il Adamu, Katsina<\/h3>\n<p>Asusun Tallafawa Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya, UNICEF, tare da ha\u0257in gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina, SUBEB, sun \u0199addamar da shirin <strong>Skills4Girls<\/strong>, wata sana\u2019o\u2019I domin yara mata da nufin bai wa \u2019yan mata matasa 35,000 a jihar Katsina dabarun sana\u2019o\u2019in dogaro da kai da kuma kasuwanci.<\/p>\n<p>Shirin, wanda ake gwajinsa a Najeriya a jihar Katsina ka\u0257ai, an \u0199addamar da shi ne ta hanyar wani taron ha\u0257in gwiwar tsara shirin da ya samu halartar \u2019yan mata matasa daga \u0199ananan hukumomin Katsina, Funtua, Kaita da Dutsi.<\/p>\n<p>Da take jawabi a wajen taron, \u0199wararriyar UNICEF kan bun\u0199asa matasa, Ngozi Izuora-Songu, ta ce an tsara shirin ne domin tabbatar da cewa \u2019yan mata sun samu \u0199warewar da za ta amfani rayuwarsu fiye da abin da suke koya a aji, tare da ba su damar bayar da gudunmawa mai kyau ga al\u2019ummominsu.<\/p>\n<p>Ta ce babban manufar shirin ita ce tabbatar da cewa \u2019yan matan sun samu \u0199warewar da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai da kuma bayar da gagarumar gudunmawa ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>A cewarta, shirin zai mayar da hankali ne kan gina \u0199warewa a fannoni uku, wa\u0257anda suka ha\u0257a da \u0199warewar samun aikin yi, kasuwanci da kuma iya samar da abubuwan amfani da kuma mayar da wani \u0253angare na abin da aka samu ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>Izuora-Songu ta bayyana cewa, yayin da wasu shirye-shirye kamar <strong>Girls Education Project (GEP)<\/strong> da <strong>REACH<\/strong> suka mayar da hankali, a wani \u0253angare, kan ci gaba da karatu da kammala makaranta, shirin Skills4Girls zai gina ne bisa nasarorin da aka samu daga wa\u0257annan shirye-shirye, tare da \u0199ara ba \u2019yan mata damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki.<\/p>\n<p>Ta ce ana gudanar da tantance \u0199warewar \u2019yan matan ne domin gano bambance-bambancen da ke tsakaninsu da kuma irin baiwar da kowannensu yake da ita.<\/p>\n<p>Ta \u0199ara da cewa ba sa son dogaro da zato wajen tsara shirin, inda za a kuma gudanar da taron ha\u0257in gwiwar tsara shirin tare da \u2019yan matan domin jin ra\u2019ayoyinsu game da irin sana\u2019o\u2019i da kasuwancin da suke son koyon su ko shiga.<\/p>\n<p>A cewarta, hakan zai taimaka wajen tsara shirin da zai dace da bu\u0199atunsu da kuma yanayin muhallin da suke rayuwa.<\/p>\n<p>Izuora-Songu ta bayyana cewa shirin zai gudana daga shekarar 2026 zuwa 2029, kuma ana sa ran zai amfani \u2019yan mata 35,000 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 19 a \u0199ananan hukumomin Katsina, Funtua, Kaita da Dutsi.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9964\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/a9ec1aac-87be-450a-a879-4d289b443e41-300x225.jpeg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/a9ec1aac-87be-450a-a879-4d289b443e41-300x225.jpeg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/a9ec1aac-87be-450a-a879-4d289b443e41-768x576.jpeg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/a9ec1aac-87be-450a-a879-4d289b443e41.jpeg 1020w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ta kuma ce \u2019yan mata masu lalura ta musamman za su samu damar shiga shirin domin tabbatar da cewa kowa ya samu dama ta bai \u0257aya wajen koyon \u0199warewar da za ta taimaka masa a rayuwa.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, shirin zai kuma shigar da samari da matasa maza 7,500, da kuma iyaye, masu ba da shawara, masu horarwa da shugabannin al\u2019umma 5,000, abin da zai kai jimillar wa\u0257anda za su amfana da horon zuwa <strong>47,500<\/strong>.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina, Dakta Kabir Gafia, ya ce hukumar za ta taka rawar da ya kamata wajen tabbatar da nasarar shirin.<\/p>\n<p>Dakta Gafia ya ce gwamnatin Jihar Katsina ta yi matu\u0199ar maraba da shirin, saboda manufofinsa sun yi daidai da ajandar gwamnatin jihar mai taken <strong>\u201cBuilding Your Future\u201d<\/strong>, wato gina makomar ku.<\/p>\n<p>Ya ce gwamnatin jihar ta kasance tana koyar da matasa da \u2019yan mata sana\u2019o\u2019i daban-daban domin su samu damar dogaro da kansu.<\/p>\n<p>Ya lissafa wasu daga cikin sana\u2019o\u2019in da shirin zai mayar da hankali a kansu, da suka ha\u0257a da sarrafay man shafawa da sabulu da sabulun wanke-wanke da turare, da kuma \u0257inki, saka, gyaran wayoyin hannu da na\u2019urorin lantarki, da kuma fasahar sadarwa da kwamfuta (ICT), da sauransu.<\/p>\n<p>Dakta Gafia ya bu\u0199aci \u2019yan mata matasa da sauran wa\u0257anda shirin ya shafa da su yi cikakken amfani da damar da shirin ya samar domin inganta rayuwarsu da makomarsu.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Isma&#8217;il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya, UNICEF, tare da ha\u0257in gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina, SUBEB, sun \u0199addamar da shirin Skills4Girls, wata sana\u2019o\u2019I domin yara mata da nufin bai wa \u2019yan mata matasa 35,000 a jihar Katsina dabarun sana\u2019o\u2019in dogaro da kai da kuma kasuwanci. Shirin, wanda ake [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9963,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2124],"class_list":["post-9962","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ilimi-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/19c4b734-13d9-429e-a330-0beb80581917.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9962","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9962"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9962\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9965,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9962\/revisions\/9965"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9963"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9962"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9962"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9962"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}