{"id":9958,"date":"2026-09-15T09:09:34","date_gmt":"2026-09-15T09:09:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9958"},"modified":"2026-09-15T09:09:44","modified_gmt":"2026-09-15T09:09:44","slug":"9958-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/9958-2\/","title":{"rendered":"NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun \u0198wayoyi Da Sata A Zamfara"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga Aminu Dalhatu, Gusau<\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru 58, Emmanuel Okonkwo, bisa zargin yin safarar wiwi, tramadol, diazepam da sauran \u0199wayoyin da doka ta hana.<\/p>\n<p>An kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2026, da misalin \u0199arfe 11:30 na dare, a shagonsa da ke yankin Bakin Tasha, \u0198aramar Hukumar Birnin Magaji ta jihar.<\/p>\n<p>Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na rundunar, ASCI Umar Mohammad, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wanda ake zargin tare da wasu wa\u0257anda ake zargi da aikata laifuka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.<\/p>\n<p>A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya shafe sama da shekaru 20 yana gudanar da wani shagon sayar da magunguna a Birnin Magaji.<\/p>\n<p>Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya ha\u0257a baki da wasu mutane biyu, wa\u0257anda ake kira Yellow da Sadiq, wa\u0257anda a yanzu haka suke tsere, wajen safarar \u0199wayoyin maye masu ha\u0257ari.<\/p>\n<p>Kayayyakin da aka \u0199wato daga hannunsa sun ha\u0257a da fakiti 112 na wiwi, allunan Exol 5 guda 1,160, sachet 14 na tramadol da allunan Diazepam D10 guda 133.<\/p>\n<p>NSCDC ta ce an mi\u0199a wanda ake zargin ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun \u0198wayoyi ta \u0198asa, NDLEA, domin ci gaba da gudanar da bincike da \u0257aukar matakin da ya dace.<\/p>\n<p>A wani labarin kuma, rundunar ta kama wasu mutane tara bisa zargin ha\u0257a baki wajen aikata laifi, lalata dukiyar jama\u2019a, barna da kuma satar kayan rufin makaranta daga Makarantar Firamare ta Tsageru da ke \u0198aramar Hukumar Tsafe.<\/p>\n<p>Umar Mohammed ya bayyana cewa Sakataren Ilimi na \u0198aramar Hukumar Tsafe, Abdulrahman Aliyu, ne ya kai rahoton lamarin ga rundunar.<\/p>\n<p>Rundunar ta ce an kama wanda ake zargi da jagorantar aikata laifin, Haruna Amadu, mai shekaru 55, \u0257an \u0199auyen Tsageru, a ranar 8 ga watan Satumba, 2026, da misalin \u0199arfe 3 na rana. Daga nan ne bincike ya kai ga gano tare da kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a lamarin.<\/p>\n<p>Ana zargin mutanen da ha\u0257a baki wajen cire kayan rufin makarantar ba tare da izinin Hukumar Ilimin Bai \u018aaya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ba.<\/p>\n<p>Rundunar ta ce wa\u0257anda ake zargin sun kuma yi \u0199o\u0199arin shawo kan hakiman gunduma da na \u0199auye domin su ba su damar shiga harabar makarantar da kwashe kayan, amma shugabannin gargajiyar sun \u0199i amincewa da bu\u0199atarsu, tare da ba su shawarar su daina aikata hakan.<\/p>\n<p><strong>Fassara; Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru 58, Emmanuel Okonkwo, bisa zargin yin safarar wiwi, tramadol, diazepam da sauran \u0199wayoyin da doka ta hana. An kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba, 2026, da misalin \u0199arfe 11:30 na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9959,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[115],"class_list":["post-9958","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/e626383b-8900-445a-8a40-2adde51ebc39.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9958","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9958"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9958\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9961,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9958\/revisions\/9961"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9959"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9958"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9958"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9958"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}