{"id":9954,"date":"2026-09-15T09:04:56","date_gmt":"2026-09-15T09:04:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9954"},"modified":"2026-09-15T09:06:04","modified_gmt":"2026-09-15T09:06:04","slug":"majalisar-dokokin-kano-ta-bu%c6%99aci-kammala-aikin-fa%c9%97a%c9%97a-ban-ruwa-na-madatsar-ruwan-watari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-dokokin-kano-ta-bu%c6%99aci-kammala-aikin-fa%c9%97a%c9%97a-ban-ruwa-na-madatsar-ruwan-watari\/","title":{"rendered":"Majalisar Dokokin Kano Ta Bu\u0199aci Kammala Aikin Fa\u0257a\u0257a Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga KHADIJAH ALIYU, Kano<\/strong><\/p>\n<p>Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin fa\u0257a\u0257a tsarin ban-ruwa na Dam \u0257in Watari da ke \u0198aramar Hukumar Bagwai.<\/p>\n<p>Wannan ya biyo bayan muhawarar da aka gudanar a zauren majalisar yayin zaman ta na yau da kullum, wanda Kakakin Majalisar, Jibril Isma\u2019il Falgore, ya jagoranta.<\/p>\n<p>Da yake gabatar da \u0199udiri kan aikin ban-ruwan Dam \u0257in Watari, \u0257an Majalisar mai wakiltar maza\u0253ar Bagwai\/Shanono, Ali Lawan Alhassan, ya ce an gina dam \u0257in ne a shekarar 1988 domin bun\u0199asa kamun kifi, shawo kan ambaliyar ruwa, ban-ruwa da kuma samar da ruwan sha ga al\u2019ummomin wasu sassan arewacin Kano.<\/p>\n<p>Dan Majalisar ya bayyana cewa Bankin Raya Musulunci ya bayar da kwangilar fa\u0257a\u0257a tsarin ban-ruwan a shekarar 2022, tare da ha\u0257in gwiwar gwamnatin Jihar Kano, \u0199ar\u0199ashin shirin bun\u0199asa noma na jihar.<\/p>\n<p>A cewarsa, an tsara aikin ne domin samar da damar yin ban-ruwa a kusan hekta 1,000 na gonaki, tare da bun\u0199asa harkokin noma tsakanin manoman yankin.<\/p>\n<p>Sai dai Ali Lawan ya nuna damuwa kan yadda aka yi watsi da aikin, inda ya ce \u0257an kwangilar ya bar wurin aikin.<\/p>\n<p>Ya ce barin aikin ya haifar da bu\u0257a\u0257\u0257un ramuka a gonaki, lamarin da ke jefa rayukan jama\u2019a cikin ha\u0257ari tare da jefa mazauna al\u2019ummomin da abin ya shafa cikin wahalhalu.<\/p>\n<p>Saboda haka, \u0257an Majalisar ya bu\u0199aci Majalisar ta kafa kwamiti domin gudanar da cikakken bincike kan aikin, ciki har da yadda aka bayar da kwangilar, tare da gabatar da shawarwarin da suka dace domin \u0257aukar matakin da ya kamata.<\/p>\n<p>\u018aan Majalisar mai wakiltar maza\u0253ar Tudun Wada, Lawan Sule Shuwaki, ne ya mara wa \u0199udirin baya.<\/p>\n<p>A wani ci gaban makamancin haka, Majalisar ta kuma bu\u0199aci gwamnatin Jihar Kano da ta gina magudanan ruwa domin samar da yanayi mafi aminci da dacewa ga mazauna garin Makera da ke mazabar Fagwalawa, \u0198aramar Hukumar Dambatta.<\/p>\n<p>\u018aan Majalisar mai wakiltar maza\u0253ar Dambatta, Murtala Musa Kore, ne ya gabatar da \u0199udirin.<\/p>\n<p>Bayan doguwar muhawara, Majalisar ta amince da \u0199udurorin biyu tare da yin kira ga gwamnatin jihar da ta \u0257auki matakan da suka dace.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin fa\u0257a\u0257a tsarin ban-ruwa na Dam \u0257in Watari da ke \u0198aramar Hukumar Bagwai. Wannan ya biyo bayan muhawarar da aka gudanar a zauren majalisar yayin zaman ta na yau da kullum, wanda Kakakin Majalisar, Jibril Isma\u2019il [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":7230,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2123],"class_list":["post-9954","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-dam"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/Abba-Kabir-Yusuf.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9954","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9954"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9954\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9957,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9954\/revisions\/9957"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7230"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9954"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9954"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9954"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}