{"id":9932,"date":"2026-09-14T12:38:38","date_gmt":"2026-09-14T12:38:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9932"},"modified":"2026-09-14T12:38:38","modified_gmt":"2026-09-14T12:38:38","slug":"adc-ta-kaddamar-da-yakin-neman-zabe-a-daura-ta-jaddada-matsayinta-kan-tallafin-man-fetur","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/adc-ta-kaddamar-da-yakin-neman-zabe-a-daura-ta-jaddada-matsayinta-kan-tallafin-man-fetur\/","title":{"rendered":"ADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Jam\u2019iyyar African Democratic Congress (ADC) ta \u0199addamar da yakin neman zabenta a shiyyar Daura ta Jihar Katsina, inda ta sake jaddada matsayinta na dawo da tallafin man fetur, sake bu\u0257e iyakokin \u0199asa na kasar nan da kuma yafe bashin karatu da aka ba \u0257alibai, game da sauran matakan da za su rage wa \u2019yan \u0199asa ra\u0257a\u0257in matsin tattalin arziki.<\/p>\n<p>Da yake jawabi ga magoya bayan jam\u2019iyyar a babban gangamin wanda aka gudanar a Daura, Shugaban Kwamitin Ya\u0199in neman Za\u0253en ADC, Alhaji Surajo Aminu Makera, ya ce wa\u0257annan manufofi za su taimaka wajen bun\u0199asa noma da masana\u2019antu tare da samar da yanayi mai kyau da zai ba tattalin arzikin \u0199asa damar farfa\u0257owa.<\/p>\n<p>\u201cIdan ADC ta kar\u0253i ragamar gwamnati a matakin tarayya, abin da zamu fara aiyanawa shine dawo da tallafin man fetur, sake bu\u0257e iyakokin \u0199asa, da kuma aiwatar da jerin manufofi da za su rage wa \u2019yan \u0199asar nan ra\u0257a\u0257i sakamakon matsin tattalin arziki .<\/p>\n<p>\u201cCire tallafin man fetur ya \u0199ara jefa harkokin noma da masana\u2019antu cikin matsala. \u0198anana da matsakaitan masana\u2019antu na shan wahala matuka, domin ku\u0257in da ya kamata su rika jujjuyawa shi suke kashewa wajen sayen man fetur, biyan haraji da kuma siyan kaya a kan farashi mai tsada.<\/p>\n<p>&#8220;Wannan ba alheri ba ne ga tattalin arziki; yana shafar samar da kaya, yana haddasa rasa aiyukan yi, sannan yana \u0199ara talauci a tsakanin &#8216;yan kasa\u201d in ji Surajo Makera.<\/p>\n<p>Ya ce idan aka ba jam&#8217;iyyar ADC dama, za ta fito da wasu manufofi da sauye-sauye da za su bun\u0199asa tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi a \u0253angaren noma da masana\u2019antu, tare da saka hannun jari a muhimman abubuwan more rayuwa kamar wutar lantarki, fasahar sadarwa ta zamani da manyan aiyuka.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9935\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260913-WA0017-1024x682-1-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260913-WA0017-1024x682-1-300x200.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260913-WA0017-1024x682-1-768x512.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260913-WA0017-1024x682-1.jpg 1024w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Surajo Makera, wanda wani jigo a jam\u2019iyyar, Alh Aliyu Mohammed Kurfi, ya wakilta a wajen taron, ya jaddada muhimmancin ha\u0257in kai, \u0257a\u2019a da kuma ci gaba da nemo magoya baya yayin ake tunkarar za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, \u0257an takarar Majalisar Dattawa karkashin tutar jam&#8217;iyyar ta ADC a shiyyar Daura, Alhaji Sani Lawal Garki, ya ce jam&#8217;iyyar zata aiwatar da manufofin da za su inganta tattalin arziki da tsaro da kuma mayar da hankali kan samun walwala ga \u0199asa.<\/p>\n<p>Ya ce matsayar jam\u2019iyyar kan dawo da tallafin man fetur, sake bu\u0257e iyakokin \u0199asa da kuma yafe bashin da ake ba \u0257alibai na daga cikin manyan tsare-tsare na rage matsin tattalin arziki ga talakawan Najeriya ke fama da shi a halin yanzu.<\/p>\n<p>Game da harkar ilimi kuwa, Sani Lawal Garki ya ce shirin jam\u2019iyyar na yafe bashin da ake bin \u0257alibai zai sauke wa daliban nauyin da ke kansu, tare da tabbatar da cewa rashin ku\u0257i bai zama kalubale ba ga samun damar yin karatun gaba da sakandare.<\/p>\n<p>Ya ce zai kuma ba manufofin ADC kan harkar tsaro muhimmanci, musamman ganin yadda \u2019yan bindiga ke shiga kananan hukumomin Kankia da Kusada wadanda ke shiyyar ta Daura, lamarin da ya danganta da rashin daukar matakan da suka kamata domin magance matsalar.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, wani jigo a jam\u2019iyyar, Alhaji Lawal Batagarawa, ya yi kira ga al&#8217;umar shiyyar Daura da su zabi mutane masu nagarta a zaben 2027, yana mai kira ga magoya bayan jam&#8217;iyyar ADC da su \u0199ara kaimi wajen wayar da kan jama\u2019a domin isar da sa\u0199on jam\u2019iyyar ga al\u2019ummomin da ke fa\u0257in shiyyar.<\/p>\n<p>A wajen taron an gabatar da tutoci ga \u2019yan takarar jam&#8217;iyyar na kujerar Dan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Dokokin Jiha.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Isma\u2019il Adamu Jam\u2019iyyar African Democratic Congress (ADC) ta \u0199addamar da yakin neman zabenta a shiyyar Daura ta Jihar Katsina, inda ta sake jaddada matsayinta na dawo da tallafin man fetur, sake bu\u0257e iyakokin \u0199asa na kasar nan da kuma yafe bashin karatu da aka ba \u0257alibai, game da sauran matakan da za su rage [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":9934,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[1323,98,839,1333,1210,2119,411],"class_list":["post-9932","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-adc","tag-daura","tag-jaddada","tag-kaddamar","tag-man-fetur","tag-tallafin","tag-zabe"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260913-WA0016-1-800x430-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9932","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9932"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9932\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9936,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9932\/revisions\/9936"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9934"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9932"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9932"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9932"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}