{"id":9925,"date":"2026-09-14T10:11:27","date_gmt":"2026-09-14T10:11:27","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9925"},"modified":"2026-09-14T10:14:13","modified_gmt":"2026-09-14T10:14:13","slug":"zamfara-ta-kara-hutun-makaranta-zuwa-makonni-biyu-saboda-cutar-mashako","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zamfara-ta-kara-hutun-makaranta-zuwa-makonni-biyu-saboda-cutar-mashako\/","title":{"rendered":"Zamfara Ta Kara Hutun Makaranta Zuwa Makonni Biyu Saboda Cutar Mashako"},"content":{"rendered":"<h1>Daga Aminu Dalhatu, Gusau<\/h1>\n<h1>Gwamnatin Jihar Zamfara ta daga ranar komawar \u0257alibai makaranta a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fa\u0257in jihar da makonni biyu, bayan shawarwarin hukumomin lafiya dangane da halin da ake ciki na cutar mashako<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar kan cutar.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Ya ce an \u0257auki wannan matakin ne domin kare lafiya da jin da\u0257in \u0257alibai da malamai da sauran al\u2019ummar makarantu.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>A cewarsa, tsawaita hutun zai ba hukumomin lafiya da na ilimi \u0199arin lokaci domin \u0199arfafa sa ido kan cutar tare da gano\u00a0 mutanen da suka yi mu\u2019amala da masu cutar da tantance bayanan allurar rigakafi da wayar da kan jama\u2019a da kuma \u0257aukar wasu matakan kariya kafin a sake bu\u0257e makarantu.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Kwamishinan ya umurci dukkan masu makarantu da shugabannin makarantu da hukumomin kula da makarantu da su bi umarnin kara kwanakin hutun.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Ya kuma bu\u0199aci makarantu su yi amfani da wannan lokacin wajen tsaftace makarantunsu ta amfani da maganin kashe \u0199wayoyin cuta a harabar makarantu yadda ya kamata, da kuma tabbatar da samar da isassun wuraren wanke hannu.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>An kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su ba hukumomin lafiya ha\u0257in kai wajen allurar rigakafi da tantance lafiyar yara da sauran matakan kariya da aka ba da shawarar \u0257auka.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Kwamishinan ya ce Ma\u2019aikatar Ilimin Kimiyya da Fasaha za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Ma\u2019aikatar lafiya domin tabbatar da samar da ingantaccen lafiya ga masu malamai da dalibai.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Bisa wannan dalilin makarantu zasu koma ne Litinin, 28 ga Satumba, 2026.<\/h1>\n<h1><\/h1>\n<h1>Gwamnatin jihar ta yaba da fahimta da ha\u0257in kan iyaye da malamai da masu makarantu da sarakunan gargajiya da\u0199ananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin ilimi.<\/h1>\n<p>Fassara: Hauwa&#8217;u Mihammed Lawal<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta daga ranar komawar \u0257alibai makaranta a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fa\u0257in jihar da makonni biyu, bayan shawarwarin hukumomin lafiya dangane da halin da ake ciki na cutar mashako Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya bayyana hakan cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9926,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[115],"class_list":["post-9925","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/f8855d8c-9b3c-4fcb-a79f-63833607a890.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9925","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9925"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9925\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9928,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9925\/revisions\/9928"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9926"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9925"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9925"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9925"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}