{"id":9896,"date":"2026-09-12T08:23:10","date_gmt":"2026-09-12T08:23:10","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9896"},"modified":"2026-09-12T16:26:13","modified_gmt":"2026-09-12T16:26:13","slug":"hukumar-alhazai-ta-jigawa-ta-nemi-karin-kujerun-hajji-na-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-alhazai-ta-jigawa-ta-nemi-karin-kujerun-hajji-na-2027\/","title":{"rendered":"Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Nemi Karin Kujerun Hajji na 2027"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Jigawa, HuUsman Muhammad Zaria\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi karin kujerun aikin Hajjin 2027 daga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), domin biyan bukatar masu niyyar zuwa aikin Hajjin daga jihar.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Ya ce hukumar ta kammala sayarwa da rajistar kujerun Hajjin da aka ware mata, inda jami\u2019an rajistar suka tabbatar da cewa an shigar da bayanan dukkan wadanda suka cika ka&#8217;idojin zuwa aikin Hajji cikin tsarin rajistar yanar gizo.<\/p>\n<p>A cewarsa, nasarar rajistar ta nuna kokarin hukumar na tabbatar da tsarin rajista mai gaskiya, inganci da tsari.<\/p>\n<p>Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce hukumar ta gabatar da bukatar karin kujeru ga NAHCON sakamakon yawan masu son zuwa aikin Hajji daga sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu an rufe kafar shigar da bayanan fasfo, yana mai cewa Kungiyar Shugabannin Hukumomin Hajji na Jihohi ta roki NAHCON da ta sake bude kafar.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar, ya bayyana fatan cewa NAHCON za ta amince da bukatar, domin bai wa karin maniyyata aikin Hajji damar kammala bayanansu.<\/p>\n<p>Ya yabawa ma\u2019aikatan hukumar bisa jajircewa da kokarin da suke yi wajen gudanar da ayyukansu, tare da kira ga maniyyatan aikin Hajjin 2027 da su rika dogaro da bayanan da hukumar ta bayar kawai domin kauce wa ya\u0257a labaran karya.<\/p>\n<p>Haka kuma, Labbo ya mika sakon ta\u2019aziyya ga NAHCON bisa rasuwar ma\u2019aikacinta a Ofishin na Shiyyar Kano, Marigayi Alhaji Salisu Gaya, wanda ya rasu ranar Juma\u2019a, 11 ga Satumba, 2026.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir\u00a0<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jigawa, HuUsman Muhammad Zaria\u00a0 Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi karin kujerun aikin Hajjin 2027 daga Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), domin biyan bukatar masu niyyar zuwa aikin Hajjin daga jihar. Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya ce hukumar ta kammala sayarwa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9898,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2113,59,2114],"class_list":["post-9896","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj2027","tag-jigawa","tag-karin-kujeru"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260912-WA0013.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9896","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9896"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9896\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9899,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9896\/revisions\/9899"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9898"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9896"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9896"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9896"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}