{"id":9860,"date":"2026-06-10T14:05:45","date_gmt":"2026-06-10T14:05:45","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9860"},"modified":"2026-06-10T14:05:45","modified_gmt":"2026-06-10T14:05:45","slug":"jigawa-ta-ware-naira-miliyan-835-don-sayen-kayan-agajin-gaggawa-saboda-ambaliya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jigawa-ta-ware-naira-miliyan-835-don-sayen-kayan-agajin-gaggawa-saboda-ambaliya\/","title":{"rendered":"Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 835 Don Sayen Kayan Agajin Gaggawa Saboda Ambaliya"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da martani na shekarar 2026, kan ku\u0257i sama da naira miliyan 835.<\/p>\n<p>Kwamishinan Ya\u0257a Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga Rediyon Najeriya a Dutse.<\/p>\n<p>Ya ce, kayayyakin da aka amince a saya sun ha\u0257a da muhimman kayan abinci na gaggawa, kayan sawa, da kuma kayan gini, domin tabbatar da gaggawar taimako idan ambaliya ta auku a sassan da ke cikin ha\u0257arin ambaliya a jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, amincewar majalisar zartarwa ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) na da nufin tabbatar da cewa za a tanadi wa\u0257annan kayan agaji a wurare masu muhimmanci domin a iya kai su cikin gaggawa duk lokacin da bukata ta taso.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, kayan abinci za su taimaka wajen magance bukatun gaggawa na abinci ga mutanen da ambaliya ta raba da muhallansu, yayin da kayan sawa da na gini za su bayar da muhimmin tallafi ga iyalan da iftila\u2019in ambaliya ya shafa.<\/p>\n<p>Sagir ya jaddada cewa, gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna jihar, musamman wa\u0257anda ke zaune a yankunan da ke fuskantar ha\u0257arin ambaliya, da su ci gaba da bin shawarwarin tsaro da hukumomin da abin ya shafa ke bayarwa.<\/p>\n<p>Ya kuma bukaci jama\u2019a da su nuna ha\u0257in kai da goyon baya ga hukumomin agajin gaggawa idan irin wannan iftila\u2019i ya faru.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da martani na shekarar 2026, kan ku\u0257i sama da naira miliyan 835. Kwamishinan Ya\u0257a Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga Rediyon Najeriya a Dutse. Ya ce, kayayyakin da aka amince [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9861,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2109,59],"class_list":["post-9860","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-agaji","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/IMG-20260214-WA0002.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9860","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9860"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9860\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9862,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9860\/revisions\/9862"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9861"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9860"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9860"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9860"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}