{"id":9855,"date":"2026-06-10T12:59:51","date_gmt":"2026-06-10T12:59:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9855"},"modified":"2026-06-10T12:59:51","modified_gmt":"2026-06-10T12:59:51","slug":"jamian-tsaro-sun-yi-nasarar-hallaka-yan-bindiga-6-a-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamian-tsaro-sun-yi-nasarar-hallaka-yan-bindiga-6-a-zamfara\/","title":{"rendered":"Jami\u2019an Tsaro Sun yi Nasarar Hallaka &#8216;Yan Bindiga 6 a Zamfara"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Rundunar \u2019Yan Sanda a Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar dakile wani hari da \u2019yan bindiga suka kai garin Kanoma da \u0199auyen Gidan Daji da ke \u0198aramar Hukumar Maru ta jihar.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce jami\u2019an tsaron ha\u0257in gwiwa sun gwabza mummunan fada da maharan, inda suka kashe shida daga cikinsu.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin \u0199arfe 11 na safe, lokacin da dimbin \u2019yan bindiga dauke da manyan makamai da suka hada da rokoki masu linzami (RPG), manyan bindigogi masu sarrafa kansu (GPMG), bindigogin harba jiragen sama da kuma bindigogin AK-47 suka mamaye yankunan.<\/p>\n<p>Bayan samun kiran gaggawa, rundunar ha\u0257in gwiwa da ta kunshi jami\u2019an \u2019yan sanda na musamman daga sashen Maru, sojoji na rundunar Operation Fansar Yamma, jami\u2019an Sashen Yaki da Manyan Laifuka (VCRU) da kuma \u2019yan sa-kai sun yi gaggawar kai dauki karkashin jagorancin DPO na yankin.<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa jami\u2019an tsaron sun yi nasarar fatattakar maharan tare da tilasta musu ja da baya.<\/p>\n<p>Ta kuma nuna cewa yayin musayar wuta, an kashe \u2019yan bindiga shida da ke kan babura biyu, yayin da wasu da dama suka tsere zuwa cikin dazuka da raunukan harbin bindiga.<\/p>\n<p>Haka kuma, an \u0199ara yawan jami\u2019an tsaro a yankin tare da \u0199addamar da sintiri mai \u0199arfi domin tabbatar da zaman lafiya mai \u0257orewa da kuma farautar wa\u0257anda suka tsere.<\/p>\n<p>Rundunar \u2019Yan Sandan Jihar Zamfara ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al\u2019umma, tare da kira ga mazauna yankin da su kasance masu sanya ido tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu Rundunar \u2019Yan Sanda a Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar dakile wani hari da \u2019yan bindiga suka kai garin Kanoma da \u0199auyen Gidan Daji da ke \u0198aramar Hukumar Maru ta jihar. A wata sanarwa da Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9856,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[2108,219,115],"class_list":["post-9855","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-jamian-tsaro","tag-yan-bindiga","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/IMG-20260610-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9855","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9855"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9855\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9858,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9855\/revisions\/9858"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9856"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9855"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9855"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9855"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}