{"id":983,"date":"2024-04-11T05:02:58","date_gmt":"2024-04-11T05:02:58","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=983"},"modified":"2024-04-11T05:04:52","modified_gmt":"2024-04-11T05:04:52","slug":"hukumar-zakka-da-wa%c6%99afi-ta-jihar-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-zakka-da-wa%c6%99afi-ta-jihar-zamfara\/","title":{"rendered":"Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta Jihar Zamfara&#8230;"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-984\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/IMG-20240411-WA0004-300x187.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"187\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/IMG-20240411-WA0004-300x187.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/IMG-20240411-WA0004-768x479.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/IMG-20240411-WA0004.jpg 1024w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta Jihar Zamfara<\/p>\n<p>Fata Ga Marasa Galihu Da Kawo Canji A Rayuwar Jama&#8217;a<\/p>\n<p>Daga Abdullahi Musa<\/p>\n<p>A \u2018yan makonnin da suka gabata ne Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta jihar Zamfara \u0199ar\u0199ashin jagorancin Sheikh Umar Ahmad Kanoma, ta bullo da wasu sabbin hanyoyi da tsare-tsaren taimaka wa wajen canja rayuwar al&#8217;umma da kyautata jin dadin da kuma zamantakewarsu.<\/p>\n<p>Hukumar ta \u0199arfafa hanyoyin da aka san ta su na jajircewa wajen yi wa al\u2019umma hidima cikin tausayi da adalci, Hukumar ta samu gagarumin ci gaba a ayyukanta na rage radadin talauci da \u0199arfafa wa marasa galihu a lokacin Azumin watan Ramadan da ya gabata.<\/p>\n<p>Bisa kulawar sakataren zartaswa, Habib Balarabe Muhammad, Hukumar ta samu gagarumar nasara wajen tallafa wa mabu\u0199ata da marasa galihu.<\/p>\n<p>Hukumar ta Kai \u0257aukin gaggawa ga mata masu fama da matsalar shaye-shayen miyagun \u0199wayoyi da haifar masu da fata a zukatansu, ta hanyar shirya masu tarukan fadakarwa da nufin kyautata rayuwarsu.<\/p>\n<p>Baya ga samar wa mata da matasa marasa galihu hanyoyin dogaro da kai, Hukumar ta tallafa masu da mahimman kayayyakin koyon sana&#8217;a da ha\u0253aka \u0199warewa a tsakaninsu. Wannan tsarin jin kai yana nuna sadaukarwar Hukumar don jindadin marasa galihu.<\/p>\n<p>A cikin watan Ramadan, Hukumar ta kara kaimi, inda ta tallafa wa mutane sama da 40,000 a fadin jihar Zamfara da kayan abinci da taimakon ku\u0257i.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, Hukumar ta samar da ga\u0253o\u0253in roba kyauta ga mutanen da rasa ga\u0253o\u0253insu sakamako hattsura ko ayyukan &#8216;yan ta&#8217;adda da taimaka wa mata masu matsalar cutar yoyon fitsari (VVF). Hakan ya jaddada himmar Hukumar wajen samun damar kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar marasa galihu.<\/p>\n<p>Ta hanyar ha\u0257in gwiwa da \u0199ungiyoyi jin kai kamar; Bright Futures Serious da Organised Crime Prevention Project (SOC), Hukumar ta samar da tsare-tsare don rigakafi da kuma tsarin tallafi, tabbatar da samari masu aikata laifuka sun sami jagoranci na gari a rayuwarsu da nufin \u0199arfafa su don kawar da aikata miyagun laifuka a tsakanin al&#8217;umma a jihar.<\/p>\n<p>Bayan Eid al-Fitr, Hukumar ta kasance mai himma, tare da yin al\u0199awarin shigar \u0257aruruwan mutane a cikin shirye-shiryen gina rayuwarsu da dabarun ha\u0253aka fasaha. Wannan tsarin sa ido yana nuna sadaukarwarsu ga \u0199arfafawa ta dogon lokaci da nufin samar da mafita mai dorewa ga al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Nasarorin da Hukumar ke samu sun nuna muhimmancin samar da kyakkyawan tsari daa irin tasirin da yake da shi. Tun daga yunkurin agajin gaggawa zuwa shirye-shiryen karfafawa na dogon lokaci, kowane aiki yana kunshe da ka&#8217;idojin hadin gwiwa da jin kai da ke cikin Zakka.<\/p>\n<p>Hukumar ta yi al\u0199awarin kiyaye \u0199a&#8217;idodin aiki, ha\u0253aka ha\u0257in gwiwa, da bullo da sabbin hanyoyi don magance talauci da kuma fuskantar \u0199alubalen tattalin arziki yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Tare da jajircewa wajen yi wa al\u2019umma hidima bisa tsarin addinin Musulunci, Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka a matsayin wata fitilar da ke haskaka rayuwar marasa galihu da kuma samar masu da fata a rayuwa.<\/p>\n<p>Fassara\/Wababe\/ Caliphate Times<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta Jihar Zamfara Fata Ga Marasa Galihu Da Kawo Canji A Rayuwar Jama&#8217;a Daga Abdullahi Musa A \u2018yan makonnin da suka gabata ne Hukumar Zakka da Wa\u0199afi ta jihar Zamfara \u0199ar\u0199ashin jagorancin Sheikh Umar Ahmad Kanoma, ta bullo da wasu sabbin hanyoyi da tsare-tsaren taimaka wa wajen canja rayuwar al&#8217;umma da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":984,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,2],"tags":[294],"class_list":["post-983","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-siyasa","tag-hajj"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/IMG-20240411-WA0004.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/983","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=983"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/983\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":986,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/983\/revisions\/986"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/984"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=983"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=983"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=983"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}