{"id":9806,"date":"2026-06-04T20:31:59","date_gmt":"2026-06-04T20:31:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9806"},"modified":"2026-06-04T20:31:59","modified_gmt":"2026-06-04T20:31:59","slug":"hukumar-alhazan-jigawa-ta-gargadi-mahajjata-kan-kayayyakin-da-aka-haramta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-alhazan-jigawa-ta-gargadi-mahajjata-kan-kayayyakin-da-aka-haramta\/","title":{"rendered":"Hukumar Alhazan Jigawa Ta Gargadi Mahajjata Kan Kayayyakin da Aka Haramta"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan Jihar Jigawa ta gargadi Alhazanta da su guji \u0257aukar kayayyakin da aka haramta a cikin jakunkunan hannu yayin dawowarsu Najeriya daga \u0199asar Saudiyya.<\/p>\n<p>Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi wannan kira a wata hira da wakilinmu Usman Mohammed Zaria a birnin Makkah na \u0199asar Saudiyya, yayin da ake shirye-shiryen dawowar Alhazan bayan kammala aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa wajibi ne Alhazai su guji sanya kayayyaki masu kaifi a cikin jakunkunansu na hannu.<\/p>\n<p>Ya ce daga cikin kayayyakin da aka haramta akwai bindigogi wasa, ko na gaske, kayayyaki masu saurin kamawa da wuta, wu\u0199a\u0199e, reza da almakashi.<\/p>\n<p>Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma gargadi Alhaza da kada su sanya ruwan Zamzam a cikin manyan jakunkunansu, haka kuma su guji \u0257aukar turare na fesawa.<\/p>\n<p>A cewarsa, kowane Alhaji yana da ha\u0199\u0199in samun lita biyar na ruwan Zamzam, don haka babu bu\u0199atar sanya shi a cikin babban akwati.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa duk Alhajin\u00a0 da ya sa\u0253a wa wannan umarni zai\u0257iya jawowa kansa matsala, domin ana gano duk kayayyakin da aka haramta yayin binciken jakunkuna, kuma hukumomi za su kwace su.<\/p>\n<p>Labbo ya bayyana cewa jiragen sama na da iyakar nauyin kayan da za su iya \u0257auka, kuma ba za su iya \u0257aukar kaya fiye da \u0199a\u2019idar da aka tanada ba.<\/p>\n<p>Saboda haka, ya bu\u0199aci Alhazan\u00a0 da su bi \u0199a\u2019idodin auna kaya domin tabbatar da dawowa cikin nasara da kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Babban Daraktan ya kuma bayyana cewa Hukumar Alhazai ta \u0198asa (NAHCON) ta amince da kamfanonin jigilar kaya domin Alhazan da ke da kayan da suka wuce \u0199a\u2019ida su yi amfani da su.<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa da zarar Alhazan sun isa Najeriya, za a mi\u0199a musu manyan jakunkunansu tare da lita biyar na ruwan Zamzam ga kowane alhaji a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan Jihar Jigawa ta gargadi Alhazanta da su guji \u0257aukar kayayyakin da aka haramta a cikin jakunkunan hannu yayin dawowarsu Najeriya daga \u0199asar Saudiyya. Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi wannan kira a wata hira da wakilinmu Usman Mohammed Zaria a birnin Makkah na \u0199asar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9807,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2029,59,991],"class_list":["post-9806","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj2026","tag-jigawa","tag-kayayyaki"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/IMG-20260604-WA0019.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9806","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9806"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9806\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9808,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9806\/revisions\/9808"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9807"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9806"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9806"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9806"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}