{"id":9790,"date":"2026-06-03T11:44:31","date_gmt":"2026-06-03T11:44:31","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9790"},"modified":"2026-06-03T11:44:31","modified_gmt":"2026-06-03T11:44:31","slug":"wani-maigadi-ya-sace-yayan-ubangidansa-a-minna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wani-maigadi-ya-sace-yayan-ubangidansa-a-minna\/","title":{"rendered":"Wani Maigadi Ya Sace &#8216;Ya&#8217;yan Ubangidansa a Minna"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aliyu Lawal<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Wani maigadi a garin Minna na Jihar Neja ya yi batan dabo da \u2019ya\u2019yan ubangidansa su biyu.<\/p>\n<p>Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Brighter da ke Minna a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da mahaifin yaran, wanda \u0257an kasuwa ne, ya kasa gano inda \u2019ya\u2019yansa Umar da Anas masu shekara shida-shida suke. Daga bisani ya fara zargin cewa Maigadin ne ya gudu da su.<\/p>\n<p>Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Danjuma, mahaifin yaran, ba ya gida a ranar Lahadi da rana. A wannan lokacin ne maigadin gidan nasa mai suna Sani Abdulrahman, ya fita da yaran domin shagulgulan Sallah a kan babur da Alhaji Danjuma ya saya masa.<\/p>\n<p>Rashin ganinsu na wani tsawon lokaci ne ya sa iyayen yaran suka fara bi asibitoci daban-daban a cikin birnin Minna, domin sun fara tunanin ko sun sami hatsari ne. Sai dai daga baya aka gano cewa yaran na hannun wa\u0257anda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.<\/p>\n<p>Da yake bayani kan lamarin, Alhaji Danjuma ya ce daga baya a wannan ranar wasu mutane sun kira shi daga dajin Erena da ke \u0198aramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, inda suka bu\u0199aci ya kawo ku\u0257in fansa domin a sako \u2019ya\u2019yansa da suke ri\u0199e da su.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja da hukumomin tsaro da su taimaka wajen tabbatar da ku\u0253utar da yaran cikin koshin lafiya. Haka kuma ya ro\u0199i al\u2019umma da su taya su addu\u2019are Allah Ya kubutar da yaran.<\/p>\n<p>Da aka tuntu\u0253i Kakakin Rundunar \u2019Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara \u0257aukar matakan gaggawa domin gano inda yaran suke da kuma ceto su.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal Wani maigadi a garin Minna na Jihar Neja ya yi batan dabo da \u2019ya\u2019yan ubangidansa su biyu. Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Brighter da ke Minna a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da mahaifin yaran, wanda \u0257an kasuwa ne, ya kasa gano inda \u2019ya\u2019yansa Umar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9792,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[2102,836,2101],"class_list":["post-9790","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-maigadi","tag-neja","tag-satar-yara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/IMG-20260603-WA0005.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9790","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9790"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9790\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9793,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9790\/revisions\/9793"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9792"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9790"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9790"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9790"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}