{"id":9783,"date":"2026-06-03T06:12:48","date_gmt":"2026-06-03T06:12:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9783"},"modified":"2026-06-03T06:24:28","modified_gmt":"2026-06-03T06:24:28","slug":"ncfbp-jigawa-ta-fara-shirin-tallafa-wa-iyalai-marasa-%c6%99arfi-da-abinci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ncfbp-jigawa-ta-fara-shirin-tallafa-wa-iyalai-marasa-%c6%99arfi-da-abinci\/","title":{"rendered":"NCFBP: Jigawa Ta Fara Shirin Tallafa wa Iyalai Marasa \u0198arfi da Abinci"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da \u0199addamar da ha\u0257in gwiwar sassa daban-daban na Shirin BankinAbinci ga Al&#8217;umma na Kasa, wato National Community Food Bank Program NCFBP, reshen shiyyar Arewa maso Yamma, wanda Uwargidan Shugaban \u0198asa, Sanata Oluremi Tinubu za ta \u0199addamar a Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko ta Gandun Sarki da ke \u0198aramar Hukumar Mallam Madori a jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta ne ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.<\/p>\n<p>A cewarsa, an \u0199ir\u0199iri wannan shiri ne domin ya\u0199i da yunwa da kuma matsalar \u0199arancin abinci mai gina jiki ga yara.<\/p>\n<p>Ya ce shirin zai taimaka wajen rage matsananciyar matsalar rashin wadataccen abinci da ke addabar marasa \u0199arfi a fa\u0257in \u0199asar nan, ta hanyar samar musu da damar samun abinci na wani \u0257an lokaci cikin tsari.<\/p>\n<p>Dakta Nura Ibrahim Kazaure ya bayyana cewa za a tantance wa\u0257anda suka cancanci cin gajiyar shirin a cibiyoyin kula da lafiya na farko, inda za a ba su takardun shaidar kar\u0253ar tallafi domin fansar kayan abinci a bankunan abinci da aka ware.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa wa\u0257anda aka fi mayar da hankali a kansu sun ha\u0257a da iyalai masu yara \u0199anana \u2018yan \u0199asa da shekara shida, da kuma mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke fuskantar ha\u0257arin rashin wadataccen abinci mai gina jiki.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya ce shirin zai kuma yi amfani da damar da \u0199asar ke da ita ta fannin noma domin tabbatar da cewa yalwar amfanin gona ta isa ga wa\u0257anda suka fi bu\u0199atarsa.<\/p>\n<p>Ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufofi 12 na Gwamna Namadi, musamman wajen tabbatar da inganta rayuwar da samar da wadatacce kuma ingantaccen abinci a jihar.<\/p>\n<p>Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta kuma jajanta wa wa\u0257anda guguwar iska da ruwan sama suka shafa a sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n<p>Majalisar ta kuma umarci Ma\u2019aikatar Jin-\u0199ai da Harkoki na Musamman da ta gaggauta kai tallafi ga wa\u0257anda lamarin ya shafa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta amince da \u0199addamar da ha\u0257in gwiwar sassa daban-daban na Shirin BankinAbinci ga Al&#8217;umma na Kasa, wato National Community Food Bank Program NCFBP, reshen shiyyar Arewa maso Yamma, wanda Uwargidan Shugaban \u0198asa, Sanata Oluremi Tinubu za ta \u0199addamar a Cibiyar Kula da Lafiya ta Farko ta Gandun Sarki da ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9785,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[59,2100],"class_list":["post-9783","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-jigawa","tag-ncfbp"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/06\/IMG-20260602-WA0018.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9783","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9783"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9783\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9787,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9783\/revisions\/9787"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9785"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9783"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9783"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9783"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}