{"id":9737,"date":"2026-05-25T20:34:51","date_gmt":"2026-05-25T20:34:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9737"},"modified":"2026-05-25T20:34:51","modified_gmt":"2026-05-25T20:34:51","slug":"hajj2026-mahajjatan-jigawa-sun-shirya-zuwa-arfa-cike-da-kwarin-gwiwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hajj2026-mahajjatan-jigawa-sun-shirya-zuwa-arfa-cike-da-kwarin-gwiwa\/","title":{"rendered":"Hajj2026: Mahajjatan Jigawa Sun Shirya Zuwa Arfa Cike da Kwarin Gwiwa"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Mahajjatan Jihar Jigawa sun fara gudanar da ibadun aikin Hajjin shekarar 2026 cikin kyakkyawan yanayi, yayin da ake jigilar su daga sansanin Mina zuwa filin Arafat.<\/p>\n<p>Aikin Hajji kan fara ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Zul-Hijja a kowace shekara, inda ake fara kai mahajjata zuwa sansanin Mina, sannan daga bisani su wuce Arafat, Muzdalifa, da Jamaratul Akaba, sannan su koma Makka domin domin yin Dawaful Ifadha.<\/p>\n<p>Yawancin mahajjatan da suka zanta da Rediyon Najeriya sun bayyana cewa duk da wahalhalun da ke tattare da gudanar da ibadun Hajji, suna da \u0199warin gwiwar gudanar da Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Wasu mahajjata daga \u0199ananan hukumomin Kirikasamma da Jahun, Alhaji Musa Yau Muhammad da Alhaji Sabitu Hussaini, sun bayyana cewa tsoron Allah da \u0199aunarsa ne ke ba su \u0199arfi da juriyar fuskantar wahalhalun Hajji, domin Allah Ya yi al\u0199awarin amsa addu\u2019o\u2019in bayinsa. Sun ce wajibi ne su jure wahalhalun saboda babu abin alheri da ke zuwa cikin sau\u0199i.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9738\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0050-225x300.jpg\" alt=\"\" width=\"225\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0050-225x300.jpg 225w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0050-768x1024.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0050.jpg 960w\" sizes=\"auto, (max-width: 225px) 100vw, 225px\" \/><\/p>\n<p>Wani mahajjaci daga Dutse, Iliya Ahmad, ya bayyana cewa Hajji \u0257aya ne daga cikin rukunan Musulunci da ya wajaba ga duk wanda yake da hali. Ya ce Al\u0199ur\u2019ani ya bayyana cewa addu\u2019o\u2019in mahajjata za su samu kar\u0253uwa.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa wannan tabbaci ka\u0257ai yana ba shi cikakken natsuwa da gamsuwa wajen fuskantar duk wani \u0199alubale da ke tattare da aikin Hajji.<\/p>\n<p>Mahajjatan sun kuma bayyana cewa kasancewarsu ba\u0199in Allah na musamman saboda amsa kiranSa da zuwa Hajji, babu wata wahala ta tafiya mai nisa, zafin rana ko cunkoso da zai hana su gudanar da wannan ibada.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9739\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0049-225x300.jpg\" alt=\"\" width=\"225\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0049-225x300.jpg 225w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0049-768x1024.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0049.jpg 864w\" sizes=\"auto, (max-width: 225px) 100vw, 225px\" \/><\/p>\n<p>Malamai sun bayyana cewa, duk wanda ya gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata, za a gafarta masa zunubansa kuma ya zama tamkar sabon jariri mara laifi.<\/p>\n<p>A wata hira da Rediyon Najeriya, Darakta Janar na Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya ce an samar da dukkan abubuwan da suka dace domin jin da\u0257in mahajjatan jihar a Arafat.<\/p>\n<p>A cewarsa, za a kai mahajjatan zuwa Dutsen Arafat cikin dare.<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cAn samar da tantuna masu na\u2019urar sanyaya iska tare da katifu, matasan kai da barguna ga kowane mahajjaci. Haka kuma saboda zafin rana, an sanya na\u2019urorin sanyaya ruwa a tsakanin tantuna domin rage ha\u0257arin rashin ruwa a jikin mahajjata.\u201d<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9740\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0048-225x300.jpg\" alt=\"\" width=\"225\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0048-225x300.jpg 225w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0048-768x1024.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0048.jpg 864w\" sizes=\"auto, (max-width: 225px) 100vw, 225px\" \/><\/p>\n<p>Labbo ya \u0199ara da cewa za a kuma samar da abinci sau uku a rana tare da ruwan sha, da lemu da \u2018ya\u2019yan itatuwa ga mahajjatan jihar.<\/p>\n<p>Ya shawarci mahajjatan da su fara da tsoron Allah a zukatansu, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko wajen gudanar da Hajji cikin sau\u0199i da nasara.<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cAnnabi (SAW) ya gudanar da Hajji ta hanyar tafiya zuwa Mina bayan fitowar rana a ranar 8 ga Zul-Hijja, amma saboda yawan mahajjata, yanzu ana fara jigilar su tun daga tsakiyar daren ranar 7 domin tabbatar da isa a lokacin da ya dace.Haka kuma ana kai su Arafat ranar 8 ga wata da daddare domin kauce wa jinkiri.\u201d<\/p>\n<p>Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, jami\u2019an Mu\u2019assasa na Saudiyya na ci gaba da gudanar da cikakken bincike ga kowane mahajjaci kafin ba shi damar shiga motocin da Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan ta Jihar Jigawa ta tanada domin kai su Dutsen Arafat.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Mahajjatan Jihar Jigawa sun fara gudanar da ibadun aikin Hajjin shekarar 2026 cikin kyakkyawan yanayi, yayin da ake jigilar su daga sansanin Mina zuwa filin Arafat. Aikin Hajji kan fara ne daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Zul-Hijja a kowace shekara, inda ake fara kai mahajjata zuwa sansanin Mina, sannan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9743,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2029,2091,59],"class_list":["post-9737","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj2026","tag-arafat","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260525-WA0047-2.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9737","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9737"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9737\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9744,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9737\/revisions\/9744"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9743"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9737"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9737"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9737"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}