{"id":9707,"date":"2026-05-24T16:40:20","date_gmt":"2026-05-24T16:40:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9707"},"modified":"2026-05-24T16:52:26","modified_gmt":"2026-05-24T16:52:26","slug":"jigawa-dubban-mahaddata-sun-halarci-taron-adduoin-zaman-lafiya-ga-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jigawa-dubban-mahaddata-sun-halarci-taron-adduoin-zaman-lafiya-ga-najeriya\/","title":{"rendered":"Jigawa: Dubban Mahaddata Sun Halarci Taron Addu\u2019o\u2019in Zaman lafiya ga Najeriya"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da addu\u2019o\u2019i na musamman domin samun zaman lafiya mai \u0257orewa, ingantaccen tsaro da \u0199arfafa ha\u0257in kan al&#8217;amurar Najeriya.<\/p>\n<p>An gudanar da taron ne a Cibiyar Horar da Ma\u2019aikata ta Manpower Development Institute da ke Dutse, inda dubban mahaddata Al-Qur\u2019ani da malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na \u0199asa suka halarta, \u0199ar\u0199ashin jagorancin Gwamna Umar Namadi.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Umar Namadi ya ce an shirya zaman addu\u2019ar ne a matsayin wani \u0253angare na tallafawa kokarin da gwamnatoci a matakai daban-daban ke aiwatarwa domin magance matsalolin tsaro da sauran \u0199alubalen da \u0199asa ke fuskanta.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa baya ga tsare-tsare da ayyukan jami\u2019an tsaro, \u0199orfafa ibada da addu\u2019o&#8217;i su ne kan gaba wajen neman zaman lafiya da kwanciyar hankali mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Malam Umar Namadi ya \u0199ara da cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ce tare da Cibiyar \u0198asa ta Mahaddatan Al-Qur\u2019ani da kuma \u0198ungiyar Mahaddatan Al-Qur\u2019ani ta Jihar Jigawa suka ha\u0257a hannu wajen shirya shirin.<\/p>\n<p>A cewarsa, mahalarta daga jihohi kusan 26 na \u0199asar nan ne suka halarci shirin, inda mahaddatan suka yi fiye da khatma 4,000 na Al-Qur\u2019ani, tare da gudanar da addu\u2019o\u2019i na musamman domin zaman lafiya, ha\u0257in kai da ci gaban Najeriya.<\/p>\n<p>Namadi ya bayyana cewa taron addu\u2019ar ya zo daidai da kwanaki goma na farkon watan Zul-Hijjah, wanda lokaci ne mai muhimmanci a addinin Musulunci, yana mai bayyana fatan cewa addu\u2019o\u2019in da aka yi za su jawo rahama da albarkar Allah SWT.<\/p>\n<p>Ya ce: &#8220;Mun za\u0253i kwanaki goma na farkon Zul-Hijjah saboda falalar da suke da ita, tare da fatan In Shaa Allah za a sami zaman lafiyamai dorewa.&#8221;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa an kuma shirya shirin ne domin tallafawa \u0199o\u0199arin gwamnatin Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu wajen ya\u0199i da rashin tsaro, \u0199arfafa ha\u0257in kan \u0199asa da bun\u0199asa ci gaban tattalin arziki.<\/p>\n<p>Gwamnan ya yabawa wadanda suka shirya taron, malaman addini da mahalarta bisa jajircewarsu da sadaukarwarsu, yana mai bayyana taron a matsayin wata alama ta kishin \u0199asa da damuwa da makomar Najeriya.<\/p>\n<p>Ya kuma bu\u0199aci \u2018yan Najeriya su ci gaba da yi wa \u0199asa addu\u2019a tare da goyon bayan shirye-shiryen gwamnati da ke da nufin samar da zaman lafiya da ci gaba.<\/p>\n<p>Taron ya \u0199unshi karatun Al-Qur\u2019ani, addu\u2019o\u2019in zaman lafiya da tsaro, da kuma addu\u2019o\u2019i na musamman ga shugabannin \u0199asa, jami\u2019an tsaro da al\u2019ummar Najeriya baki \u0257aya.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da addu\u2019o\u2019i na musamman domin samun zaman lafiya mai \u0257orewa, ingantaccen tsaro da \u0199arfafa ha\u0257in kan al&#8217;amurar Najeriya. An gudanar da taron ne a Cibiyar Horar da Ma\u2019aikata ta Manpower Development Institute da ke Dutse, inda dubban mahaddata Al-Qur\u2019ani da malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na \u0199asa suka halarta, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9709,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1344,2087,280,2086,20,50],"class_list":["post-9707","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-adduoi","tag-halarci","tag-lafiya","tag-mahaddata","tag-najeriya","tag-taro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260524-WA0033.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9707","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9707"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9707\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9708,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9707\/revisions\/9708"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9709"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9707"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9707"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9707"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}