{"id":9700,"date":"2026-05-23T20:21:15","date_gmt":"2026-05-23T20:21:15","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9700"},"modified":"2026-05-23T20:21:15","modified_gmt":"2026-05-23T20:21:15","slug":"hajj2026-mahajjata-sun-fara-tururuwa-a-kasuwannin-makka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hajj2026-mahajjata-sun-fara-tururuwa-a-kasuwannin-makka\/","title":{"rendered":"Hajj2026: Mahajjata Sun Fara Tururuwa a Kasuwannin Makka"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya da ake sa ran za su fara gudanar da ibadun aikin Hajji nan da ranar 25 ga watan Mayu, sun mamaye shaguna da manyan kasuwanni domin sayen tsaraba ga &#8216;yan uwansu da abokan arziki.<\/p>\n<p>Wakilinmu Usman Mohammed Zaria daga Makkah ya ruwaito cewa, ya zama al&#8217;ada ga mafi yawan mahajjata su sayi tsaraba yayin aikin Hajji, saboda ana ganin duk wata kyauta daga \u0199asa mai tsarki tana da muhimmanci da kuma armashi na musamman.<\/p>\n<p>Mahajjatan na sayen tsarabe-tsarabe iri-iri da suka ha\u0257a da tufafi, takalma, jakunkuna, turare, dabino, kayan wasa, darduma, kayan ado da kuma kayayyakin amfanin gida da sauransu.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin mahajjatan, Alhaji Abdullahi Ibrahim da Alhaji Salisu Ismail daga Malam Madori, sun ce kasancewar wannan ne Hajjinsu na farko, dukkan &#8216;yan uwansu na sa ran samun tsaraba daga gare su.<\/p>\n<p>Sun ce, Kyaututtukan za su bambanta gwargwadon kusancinsu da, &#8220;<em>ba za a rasa abin da za a bada tsaraba ga masoya ba komin kankantarta<\/em>&#8220;. In ji su.<\/p>\n<p>Sun kuma bayyana cewa daga cikin Dala 500 da aka ba su a matsayin ku\u0257in tafiya, sun tanadi \u0199arin kudade tun kafin zuwansu \u0199asa mai tsarki domin sayayya ta kansu da kuma tsaraba.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9701\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0040-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0040-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0040-1024x768.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0040-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0040.jpg 1152w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Wani mahajjaci, Alhaji Mubarak Musa Adamu daga \u0199aramar hukumar Dutse, ya ce sayen tsaraba ga masoya da &#8216;yan uwa abu ne mai matu\u0199ar muhimmanci, ko da kuwa ba Hajjin farko ba ne.<\/p>\n<p>Ya ce, &#8220;<em>Mutane suna daraja tsarabar da aka kawo daga Saudiyya, ko da dabino ne ko darduma ka saya musu, suna matu\u0199ar jin da\u0257i saboda muhimmancin da ake danganta ta da \u0199asa mai tsarki<\/em>.&#8221;<\/p>\n<p>Mahajjatan na yawan zuwa manyan kasuwanni da shaguna, yayin da wasu suke sayayya a bakin tituna.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin mahajjatan sun ce suna samun gamsuwa da kwanciyar hankali idan suna sayayya a manyan kasuwanni duk da tsadar kayayyaki, inda suka ce tsananin zafi da cunkoson jama&#8217;a na sanya yin sayayya a bakin hanya ya zama da wahala.<\/p>\n<p>Sun ce, &#8220;Farashin kayayyaki a manyan otal-otal da kasuwanni yana da tsada, &#8216;<em>amma ba mu damu ba saboda muna samun gamsuwa kuma shagunan suna da na&#8217;urar sanyaya wuri.<\/em>&#8221;<\/p>\n<p>An kammala dukkan shirye-shirye domin fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 wanda zai gudana na tsawon kwanaki hu\u0257u.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria\u00a0 Mahajjata daga sassa daban-daban na duniya da ake sa ran za su fara gudanar da ibadun aikin Hajji nan da ranar 25 ga watan Mayu, sun mamaye shaguna da manyan kasuwanni domin sayen tsaraba ga &#8216;yan uwansu da abokan arziki. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria daga Makkah ya ruwaito cewa, ya zama [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9702,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2029,2084,757,2085],"class_list":["post-9700","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj2026","tag-kasuwanni","tag-mahajjata","tag-tsaraba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260523-WA0037.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9700","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9700"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9700\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9703,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9700\/revisions\/9703"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9702"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9700"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9700"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9700"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}