{"id":9660,"date":"2026-05-20T11:40:17","date_gmt":"2026-05-20T11:40:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9660"},"modified":"2026-05-20T11:46:45","modified_gmt":"2026-05-20T11:46:45","slug":"kano-hukumar-hisbah-ta-yi-karin-girma-ga-kwamandojin-kananan-hukumomi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kano-hukumar-hisbah-ta-yi-karin-girma-ga-kwamandojin-kananan-hukumomi\/","title":{"rendered":"Kano: Hukumar Hisbah Ta yi Karin Girma ga Kwamandojin Kananan Hukumomi"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa kwamandojinta na Kananan Hukumomin jihar 44 karin matsayi a wani biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar.<\/p>\n<p>Da yake jawabi yayin bikin karin matsayi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Aminu Daurawa, ya bayyana cewa an yi karin matsayin ne bisa la\u2019akari da jajircewa, himma da kuma kwazon jami\u2019an wajen gudanar da ayyukansu.<\/p>\n<p>Daurawa ya bukaci kwamandojin da aka yi wa karin matsayi su kara kaimi tare da inganta ayyukansu domin tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar wannan karin matsayi.<\/p>\n<p>Jami\u2019an da a baya suke da mukamin Mataimakan Sufuritanda (Assistant Superintendents), an daga su zuwa mukamin Sufuritandan Hisbah (Hisbah Superintendents).<\/p>\n<p>Babban Kwamandan ya kuma shawarci jami\u2019an da aka yi wa karin matsayin da su kasance masu nuna kwarewa da hakuri yayin gudanar da ayyukansu, tare da guje wa duk wani abu da ka iya bata martaba ko mutuncin hukumar.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a madadin wadanda aka yi wa karin matsayi, Hamidan Tanko, wanda shi ne Kwamandan Karamar Hukumar Municipal kuma Shugaban Dandalin Kwamandojin Hisbah na Kananan Hukumomi 44, ya nuna godiya ga shugabannin hukumar bisa wannan karin matsayi.<\/p>\n<p>Ya bayyana karin matsayin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma ya dace, tare da kira ga abokan aikinsa da su ci gaba da nuna gaskiya, aiki tukuru, rikon amana da sadaukarwa wajen gudanar da aiki.<\/p>\n<p>Daga cikin wadanda suka taimaka wa Babban Kwamandan wajen bikin sanya sabbin mukamai akwai Mukaddashin Babban Kwamanda Mujahid Aminuddeen Abubakar, Khadija Sagir Suleman da sauran manyan jami\u2019an hukumar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu\u00a0 Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa kwamandojinta na Kananan Hukumomin jihar 44 karin matsayi a wani biki da aka gudanar a hedikwatar hukumar. Da yake jawabi yayin bikin karin matsayi, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Aminu Daurawa, ya bayyana cewa an yi karin matsayin ne bisa la\u2019akari da jajircewa, himma da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9662,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[122,39,636],"class_list":["post-9660","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hisbah","tag-kano","tag-karin-girma"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/Hisbah-CG.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9660","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9660"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9660\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9665,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9660\/revisions\/9665"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9662"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9660"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9660"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9660"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}