{"id":9656,"date":"2026-05-19T07:28:03","date_gmt":"2026-05-19T07:28:03","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9656"},"modified":"2026-05-19T07:28:03","modified_gmt":"2026-05-19T07:28:03","slug":"rundunar-yan-sandan-taraba-ta-cafke-wanda-ake-zargi-da-damfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/rundunar-yan-sandan-taraba-ta-cafke-wanda-ake-zargi-da-damfara\/","title":{"rendered":"Rundunar \u2019Yan Sandan Taraba Ta Cafke Wanda Ake Zargi Da Damfara"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019Yan Sandan Jihar Taraba ta sanar da al\u2019umma kama wani da ake zargi da aikata laifukan sojan gona da damfara da kuma kar\u0253ar ku\u0257i ta hanyar yaudara, inda yake ikirarin yana da ala\u0199a da Ofishin Gwamnan Jihar Taraba.<\/p>\n<p>Hakan na \u0199unshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na rundunar mai ri\u0199on mu\u0199ami, ASP Victor Mshelizah, ya sanya wa hannu.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce, a ranar 12 ga watan Mayun 2026 da misalin \u0199arfe 11:30 na safe, mataimakin jami\u2019in tsaron Gwamnan Jihar Taraba (ADC) ya samu sahihan bayanai cewa wasu mutane marasa gaskiya na amfani da sunansa da ofishinsa wajen bata masa suna tare da damfarar \u2019yan siyasa da sauran jama\u2019a a jihar.<\/p>\n<p>Ta ce bayan samun bayanan sirrin, jami\u2019an tsaro suka fara bincike domin gano tare da cafke wa\u0257anda ke da hannu a cikin ayyukan damfarar.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, bayan gudanar da bincike mai zurfi, an kama wani mai suna Seth Samuel Sule, mazaunin unguwar Magami a \u0199aramar hukumar Jalingo ta jihar Taraba, bisa zargin hannu a lamarin.<\/p>\n<p>A yayin tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa da kansa, inda ya bayyana cewa tsakanin \u0199arshen watan Afrilun 2026 zuwa farkon watan Mayun 2026, ya yi amfani da wata lambar waya wajen kwaikwayon ADC na gwamnan jihar Taraba.<\/p>\n<p>Har ila yau, wanda ake zargin ya amsa cewa ya damfari wani mutum ku\u0257i har Naira miliyan 1 da dubu 320, ta hanyar yi masa al\u0199awarin taimaka masa wajen samun tikitin takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a jam\u2019iyyar APC, wanda daga baya aka gano cewa yaudara ce.<\/p>\n<p>Rundunar ta ce har yanzu bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken.<\/p>\n<p>Rundunar \u2019yan sandan jihar Taraba ta garga\u0257i jama\u2019a da su yi hattara da mutanen da ke ikirarin su jami\u2019an gwamnati ne ko kuma suna da ala\u0199a da masu ri\u0199e da mu\u0199aman gwamnati domin damfarar mutane.<\/p>\n<p>Ta kuma shawarci jama\u2019a da su ri\u0199a tantance duk wata mu\u2019amala mai muhimmanci ko ikirarin siyasa ta hanyoyin hukuma kafin su bayar da ku\u0257i ko yin wata yarjejeniya.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199are da cewa rundunar \u2019yan sandan jihar Taraba \u0199ar\u0199ashin jagorancin kwamishinan \u2019yan sanda, CP Morkwap Sebastian Dongshal, na ci gaba da jajircewa wajen ya\u0199i da duk wani nau\u2019in damfara da aikata laifuka a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Daga Sani Sulaiman.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019Yan Sandan Jihar Taraba ta sanar da al\u2019umma kama wani da ake zargi da aikata laifukan sojan gona da damfara da kuma kar\u0253ar ku\u0257i ta hanyar yaudara, inda yake ikirarin yana da ala\u0199a da Ofishin Gwamnan Jihar Taraba. Hakan na \u0199unshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na rundunar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9657,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1054],"class_list":["post-9656","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-damfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/448516e7-1a39-4325-b3aa-ffe47cf216fe.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9656","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9656"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9656\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9658,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9656\/revisions\/9658"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9657"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9656"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9656"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9656"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}