{"id":9567,"date":"2026-05-13T14:30:28","date_gmt":"2026-05-13T14:30:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9567"},"modified":"2026-05-13T14:30:28","modified_gmt":"2026-05-13T14:30:28","slug":"mai-alfarma-sarkin-musulmi-ya-nemi-a-gaggauta-hukunta-masu-safarar-yara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/mai-alfarma-sarkin-musulmi-ya-nemi-a-gaggauta-hukunta-masu-safarar-yara\/","title":{"rendered":"Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Nemi a Gaggauta Hukunta Masu Safarar Yara"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Nasiru Malali<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Dr Muhammad Sa&#8217;ad Abubakar NSCIA, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an gaggauta gurfanar da masu safarar yara da masu aikata cin zarafin jinsi domin rage wannan matsala.<\/p>\n<p>Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a Sokoto yayin bikin cika shekaru 20 da kafuwar Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa, NAPTIP, reshen shiyyar Sokoto. Ya ce jinkirin tabbatar da adalci na kara wa masu aikata irin wadannan laifuka karfin guiwar ci gaba da munanan ayyukan.<\/p>\n<p>Dr Sa&#8217;ad Abubakar, wandaSarkin Yakin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabi ya wakilta,\u00a0 ya jaddada cewa ya zama wajibi iyaye su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu duk kuwa da halin da ake ciki.<\/p>\n<p>A sakonsa na fatan alherin, Kwamandan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, a jihar Sokoto, Mustapha Gidado, ya roki NAPTIP da ta taimaka wajen tsaftace jihar Sokoto, ta hanyar tabbatar da aiwatar da Dokar Kare Hakkin Yara, musamman ta hanyar hukunta iyayen da ke barin \u2018ya\u2019yansu suna yawo kan tituna suna bara da sunan almajiranci.<\/p>\n<p>Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa ake ganin ana jinkirta tabbatar da adalci, Babban Alkalin Jihar Sokoto, Justice Mohammed Saidu Sifawa, wanda Babban Magatakardar Kotun jihar, Aliyu Jafar Mohammed, ya wakilta, ya ce akwai dalilai da dama da ke haddasa jinkirin da wasu ke gani.<\/p>\n<p>A cewarsa, gaggauta shari\u2019a ba tare da bin ka\u2019ida ba na iya haifar da rashin adalci, saboda doka ta tanadi bai wa duk wanda ake tuhuma damar kare kansa cikin adalci, baya ga jinkirin da ake samu daga matakan shigar da kara, bincike da sauran hanyoyin shari\u2019a da sai an bi cikin tsanaki.<\/p>\n<p>Babban Alkalin ya kara da cewa NAPTIP babbar abokiyar hulda ce wajen gudanar da harkokin shari\u2019a.<\/p>\n<p>A nata jawabin, Darakta Janar ta NAPTIP, Hajiya Binta Lami Bello, wadda Misbau Iya Kaura ya wakilta, ta tabbatar da cewa hukumar ta gudanar da bincike tare da samun nasarar hukunta masu laifukan safarar mutane da dama, lamarin da ke zama babban darasi ga sauran masu niyyar aikata irin wadannan laifuka.<\/p>\n<p>Ta ce hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, masarautu, shugabannin addini da na al\u2019umma, da kuma kungiyoyin ci gaba da na fararen hula, ya taimaka sosai wajen musayar bayanan sirri, tallafawa wadanda abin ya shafa da kuma samar da tsare-tsaren hadin gwiwa wajen yaki da safarar mutane a yankin Sokoto.<\/p>\n<p>Darakta Janar din ta kuma yi kira da gwamnatin jihar Sokoto da ta kafa Kwamitin Yaki da Safarar Mutane, ganin cewa ana amfani da jihar a matsayin hanyar fitar da mutane zuwa wasu wurare.<\/p>\n<p>Taron mai taken, \u201c<strong><em>Shekaru 20 na Gaskiya, Kwarin Gwiwa da Adalci: Karfafa Hadin Gwiwa Domin Yaki da Safarar Mutane da Cin Zarafin Jama\u2019a<\/em><\/strong>,\u201d ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na rayuwa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Nasiru Malali Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Dr Muhammad Sa&#8217;ad Abubakar NSCIA, ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an gaggauta gurfanar da masu safarar yara da masu aikata cin zarafin jinsi domin rage wannan matsala. Sarkin Musulmin ya yi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9568,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1613,785,131,295],"class_list":["post-9567","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-naptip","tag-safarar-yara","tag-sarkin-musulmi","tag-sokoto"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260513-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9567","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9567"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9567\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9569,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9567\/revisions\/9569"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9568"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9567"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9567"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9567"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}