{"id":9544,"date":"2026-05-12T09:19:08","date_gmt":"2026-05-12T09:19:08","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9544"},"modified":"2026-05-12T09:19:08","modified_gmt":"2026-05-12T09:19:08","slug":"cibiyar-ku%c9%97i-ta-yi-alkawarin-ha%c9%97in-gwiwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/cibiyar-ku%c9%97i-ta-yi-alkawarin-ha%c9%97in-gwiwa\/","title":{"rendered":"Cibiyar Ku\u0257i Ta Yi Alkawarin Ha\u0257in Gwiwa"},"content":{"rendered":"<p>Cibiyar koyar da dabarun tsara harkokin ku\u0257i domin dorewar tattalin arziki ta sake jaddada aniyarta na ha\u0257a kai da gwamnati da majalisun dokoki domin inganta yadda ake tafiyar da ku\u0257a\u0257en jama\u2019a a Najeriya.<\/p>\n<p>Daraktan Janar na cibiyar, Farfesa Abdullahi Ya\u2019u, ya bayyana haka yayin taron masu tsara harkokin ku\u0257i na Afirka da aka gudanar a Abuja. Ya ce cibiyar na zuba jari sosai wajen bincike da ci gaba domin bun\u0199asa harkokin ku\u0257i a matakin \u0199asa da na \u0199ananan al\u2019umma.<\/p>\n<p>Ya ce cibiyar na \u0199addamar da wani babban shiri mai suna \u201c Shirin Bada Fifiko akan \u2018yan kasa, wanda ya \u0199unshi bu\u0199atu da gibin ci gaba da al\u2019ummomin \u0199ananan hukumomi 774 na \u0199asar nan ke da su.<\/p>\n<p>Farfesa Abdullahi Ya\u2019u ya bayyana cewa an gudanar da bincike mai zurfi domin gano matsaloli da bu\u0199atun al\u2019umma a dukkan \u0199ananan hukumomin \u0199asar. Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da shugabanni sun cika al\u0199awuran da suka \u0257auka ga jama\u2019a.<\/p>\n<p>A cewarsa, shekaru da dama ana gudanar da za\u0253e tare da al\u0199awuran baka ba tare da rubutattun yarjejeniyoyi tsakanin shugabanni da al\u2019umma ba. Ya ce wannan sabon tsarin zai bai wa jama\u2019a damar sanin ayyukan da \u2018yan siyasa suka yi alkawarin aiwatarwa idan sun samu mulki.<\/p>\n<p>Daraktan Janar \u0257in ya ce \u0199wararru na da muhimmiyar rawa wajen sake fasalin yadda ake raba albarkatu da tafiyar da su domin cigaban \u0199asa. Ya \u0199ara da cewa za a samar da takardun ga dukkan \u0199ananan hukumomi domin jama\u2019a su amfana da su.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa ana son kowace al\u2019umma ta cimma matsaya da masu neman mu\u0199ami kan irin ayyukan da za su aiwatar idan suka hau mulki, domin kawo \u0199arshen al\u0199awuran da ba sa haifar da sakamako.<\/p>\n<p>Masu halartar taron sun nuna kwarin gwiwa cewa cibiyar za ta taimaka wajen inganta rayuwar \u2018yan Najeriya. Haka kuma, mai kula da cibiyar, Husaini Sani Abubakar, ya yi al\u0199awarin ha\u0257a \u0199ananan sana\u2019o\u2019i cikin tsarin tattalin arziki domin bun\u0199asa arzikin \u0199asa.<\/p>\n<p>Bashir Mayere\/Abuja<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cibiyar koyar da dabarun tsara harkokin ku\u0257i domin dorewar tattalin arziki ta sake jaddada aniyarta na ha\u0257a kai da gwamnati da majalisun dokoki domin inganta yadda ake tafiyar da ku\u0257a\u0257en jama\u2019a a Najeriya. Daraktan Janar na cibiyar, Farfesa Abdullahi Ya\u2019u, ya bayyana haka yayin taron masu tsara harkokin ku\u0257i na Afirka da aka gudanar a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9545,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,1,11],"tags":[425],"class_list":["post-9544","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-abuja"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/97cca8f0-0e86-45cf-8058-ddcd5532ebca.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9544","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9544"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9544\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9546,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9544\/revisions\/9546"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9545"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9544"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9544"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9544"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}