{"id":9436,"date":"2026-05-04T15:15:23","date_gmt":"2026-05-04T15:15:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9436"},"modified":"2026-05-04T15:15:23","modified_gmt":"2026-05-04T15:15:23","slug":"ndlea-ta-kama-mutane-6-da-ake-zargi-da-tuammali-da-miyagun-kwayoyi-a-harabar-buk","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ndlea-ta-kama-mutane-6-da-ake-zargi-da-tuammali-da-miyagun-kwayoyi-a-harabar-buk\/","title":{"rendered":"NDLEA Ta Kama Mutane 6 da Ake Zargi da Tu&#8217;ammali da Miyagun Kwayoyi a Harabar BUK"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Abdullahi Jalaluddeen<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta \u0198asa (NDLEA), reshen Kano, ta kai samame yankin\u00a0 Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK), inda ta kama mutane shida da ake zargi da safarar miyagun \u0199wayoyi tare da rusa wasu wuraren da ake zargin ana yin wannan haramtacciyar harka.<\/p>\n<p>Mai magana da yawun hukumar a Kano, ASN Sadiq Maigatari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.<\/p>\n<p>Ya ce an gudanar da aikin ne \u0199ar\u0199ashin jami\u2019an \u201cOperation Sharar Mafaka\u201d, bayan samun \u0199orafi daga shugabancin Jami\u2019ar\u00a0 kan yadda wasu mutane ke amfani da sassan harabar jami\u2019ar da kewayenta wajen saye da sayar da miyagun \u0199wayoyi da kuma shan su.<\/p>\n<p>A yayin samamen, jami\u2019an NDLEA sun kama mutane shida da aka bayyana a matsayin masu shiga harabar ba bisa ka\u2019ida ba, tare da kwace wasu abubuwa da ake dangantawa da harkar miyagun \u0199wayoyi, sannan aka lalata su.<\/p>\n<p>Kwamandan NDLEA na Kano, CN DY Lawal, ya ce wannan aiki na nuna \u0199udirin hukumar na tabbatar da tsaftataccen muhalli mai aminci ga \u0257alibai, ma\u2019aikata da mazauna yankin jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa hukumar za ta ci gaba da wannan aiki na \u201cOperation Sharar Mafaka\u201d domin ganowa da tarwatsawa tare da kar\u0253e wuraren da ake amfani da su wajen aikata laifukan miyagun \u0199wayoyi a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>NDLEA ta kuma yaba wa shugabancin jami\u2019ar bisa ha\u0257in kai, tana mai cewa saurin kai rahoton ya taimaka wajen gaggauta daukar mataki mai inganci kan matsalar tsaro.<\/p>\n<p>Haka kuma hukumar ta yi garga\u0257i ga jama\u2019a da su guji amfani da cibiyoyin gwamnati ko wuraren jama\u2019a wajen harkokin miyagun \u0199wayoyi, tare da kira ga jama\u2019a da su ri\u0199a bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen bankado sauran hanyoyin masu safarar miyagun \u0199wayoyi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Abdullahi Jalaluddeen Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta \u0198asa (NDLEA), reshen Kano, ta kai samame yankin\u00a0 Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK), inda ta kama mutane shida da ake zargi da safarar miyagun \u0199wayoyi tare da rusa wasu wuraren da ake zargin ana yin wannan haramtacciyar harka. Mai magana da yawun hukumar a Kano, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9438,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[736,900,489],"class_list":["post-9436","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-buk","tag-kwayoyi","tag-ndlea"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0026.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9436","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9436"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9436\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9439,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9436\/revisions\/9439"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9438"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9436"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9436"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9436"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}