{"id":9413,"date":"2026-05-04T13:17:33","date_gmt":"2026-05-04T13:17:33","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9413"},"modified":"2026-05-04T13:21:32","modified_gmt":"2026-05-04T13:21:32","slug":"rukunin-farko-na-alhazan-jihar-kebbi-ya-isa-kasa-mai-tsarki","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/rukunin-farko-na-alhazan-jihar-kebbi-ya-isa-kasa-mai-tsarki\/","title":{"rendered":"Rukunin Farko na Alhazan Jihar Kebbi ya Isa Kasa Mai Tsarki"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Sani Dutsinma\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi bankwana da rukuni na farko na maniyyata 418 daga jihar da suka tashi\u00a0 zuwa \u0199asar Saudiyya domin fara aikin Hajjin shekarar 2026.<\/p>\n<p>Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tashinsu a Filin Jirgin Sama na Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, Gwamna Idris ya nuna godiya ga Allah Ma\u0257aukakin Sarki da Ya ba su damar halartar aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Gwamna Nasir Idris ya bu\u0199aci su kasance jakadu nagari na jihar da ma Najeriya gaba \u0257aya a duk tsawon zamansu a \u0199asa mai tsarki, tare da yin kira a garesu da su yi addu\u2019ar zaman lafiya a Jihar Kebbi da \u0199asa baki \u0257aya.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9415\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-300x200.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-1024x682.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-768x512.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-1536x1024.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0016-2048x1365.jpg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Jirgi na farko ya tashi ne da yammacin ranar Lahadi, \u0257auke da maniyyata 418 daga \u0199ananan hukumomin Aliero, Koko\/Besse, Bunza da Kalgo, tare da jami\u2019an Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kebbi.<\/p>\n<p>Ya tabbatar wa maniyyatan da ingantattun tsare-tsaren jin da\u0257i, ciki har da samar da mafi kyawun masauki kusa da Masallacin Harami da ke Makka, abinci mai kyau da kuma biya musu Hadaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa na da \u0199udirin tabbatar da jin da\u0257i da kare mutuncin dukkan alhazai.<\/p>\n<p>Gwamna Idris ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ci gaba da al\u2019adar tallafawa alhazai ta hanyoyi daban-daban, ciki har da \u0257aukar nauyin Hadaya, da kuma samar da sufuri kyauta domin gudanar da Ziyarah a Madina.<\/p>\n<p>Yayin da ya yi kira ga masu ri\u0199e da mu\u0199aman siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka wa alhazai daga yankunansu, ya kuma bu\u0199aci maniyyatan su sadaukar da kansu ga addu\u2019o\u2019i domin Jihar Kebbi da Najeriya, musamman a filin Arafat.<\/p>\n<p>Tun da farko, Shugaban Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruk Musa Enabo, ya yaba wa Gwamnan bisa irin goyon bayan da yake bai wa alhazai. Ya bayyana muhimman matakan da aka \u0257auka kamar biyan ku\u0257in Hadaya, inganta tsarin abinci da kuma samar da masauki mai inganci a Makka.<\/p>\n<p>A jawabansu daban-daban, Malam Lawal Baiti Mai Kwalta da Malam Abubakar Atiku Walin Kalgo sun yi wa\u2019azi kan wajibcin aikin Hajji tare da jan hankalin maniyyata da su kiyaye ladabi, gaskiya da sadaukarwa a duk tsawon aikin ibadar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Sani Dutsinma\u00a0 Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi bankwana da rukuni na farko na maniyyata 418 daga jihar da suka tashi\u00a0 zuwa \u0199asar Saudiyya domin fara aikin Hajjin shekarar 2026. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tashinsu a Filin Jirgin Sama na Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, Gwamna Idris ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9414,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1906,139,2052],"class_list":["post-9413","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-2026hajj","tag-kebbi","tag-rukunin-farko"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/IMG-20260504-WA0015.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9413","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9413"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9413\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9418,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9413\/revisions\/9418"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9414"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9413"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9413"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9413"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}