{"id":9390,"date":"2026-04-30T08:28:51","date_gmt":"2026-04-30T08:28:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9390"},"modified":"2026-04-30T08:28:51","modified_gmt":"2026-04-30T08:28:51","slug":"ncc-ta-umarci-kamfanonin-sadarwa-su-biya-diyya-ga-wasu-yan-nijeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ncc-ta-umarci-kamfanonin-sadarwa-su-biya-diyya-ga-wasu-yan-nijeriya\/","title":{"rendered":"NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Biya Diyya Ga Wasu &#8216;Yan Nijeriya"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar kula da kamfanonin Sadarwa ta kasa ta umurci kamfanonin sadarwar wayar hannu a Najeriya da su biya diyya ga kwastomomin da suka fuskanci matsalar rashin ingancin sadarwa a yankunan da kamfanonin suka kasa cika ka\u2019idojin ingancin sadarwa da aka gindaya.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da shugabar sashen hul\u0257a da jama\u2019a ta hukumar, Nnenna Ukoha ta sanya wa hannu, an ce wannan umarni ya wajabta wa kamfanonin sadarwar su biya diyya kai tsaye ga masu amfani idan an samu gazawa wajen cika ma\u2019aunin ingancin sadarwa.<\/p>\n<p>Hukumar ta bayyana cewa za a bayar da wannan diyya ne ta hanyar \u0199arin ku\u0257in kira, wanda za a \u0199ididdige bisa la\u2019akari da yadda masu amfani ke kashe ku\u0257i a matsakaici da kuma kasancewarsu a \u0199ananan hukumomin da aka samu matsalar sadarwar a cikin wani takamaiman lokaci.<\/p>\n<p>NCC ta ce wannan mataki wani \u0253angare ne na \u0199o\u0199arinta na kare ha\u0199\u0199in masu amfani da sadarwa tare da tabbatar da cewa ba su ne za su \u0257auki nauyin matsalolin da suka samo asali daga gazawar kamfanonin sadarwa ba.<\/p>\n<p>A cewar hukumar, harkokin sadarwa suna taka muhimmiyar rawa wajen bun\u0199asa tattalin arziki, hul\u0257ar jama\u2019a da kuma samun damar cin gajiyar fasahar zamani, kuma rashin ingancin sadarwa na yin illa ga ayyukan yau da kullum, kasuwanci da kuma amincewar jama\u2019a ga tsarin sadarwa.<\/p>\n<p>Hukumar ta \u0199ara da cewa duk da cewa tara na daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen hukunta kamfanonin da suka gaza samar da ingantaccen sadarwa, sabon matakin ya fi mayar da hankali ne kan kare muradun masu amfani tare da \u0199ara \u0257ora alhakin inganta sadarwa kan kamfanonin sadarwa.<\/p>\n<p>Baya ga wannan umarni na biyan diyya, NCC ta kuma umurci kamfanonin dake kula da turakun \u00a0sadarwa da ke da alhakin kula da muhimman kayan aikin sadarwa kamar turakun da su zuba jari wajen inganta kayan aikin sadarwa ta hanyar amfani da ku\u0257a\u0257en tarar da aka ci su, tare da wasu \u0199arin matakan tara da hukumar za ta \u0257auka.<\/p>\n<p>NCC ta jaddada cewa dole ne kamfanonin sadarwa su ci gaba da zuba jari wajen \u0199arfafa tsarin sadarwa, fa\u0257a\u0257a \u0199arfin aiki da inganta kayayyakin more rayuwa domin biyan bu\u0199atun da ke \u0199aruwa a fannin sadarwa.<\/p>\n<p>Hukumar ta ce za ta ci gaba da amfani da matakan sa ido da doka domin tabbatar da adalci, gaskiya da \u0257ora alhaki a fannin sadarwa, tare da tabbatar da cewa duk masu amfani da layukan sadarwa suna samun ingantaccen sadarwa da ya dace da bun\u0199asar tattalin arzikin dijital na Najeriya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Hukumar kula da kamfanonin Sadarwa ta kasa ta umurci kamfanonin sadarwar wayar hannu a Najeriya da su biya diyya ga kwastomomin da suka fuskanci matsalar rashin ingancin sadarwa a yankunan da kamfanonin suka kasa cika ka\u2019idojin ingancin sadarwa da aka gindaya. A cikin wata sanarwa da shugabar sashen hul\u0257a da jama\u2019a ta hukumar, Nnenna [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9391,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1443],"class_list":["post-9390","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ncc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/NCC-logo.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9390","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9390"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9390\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9392,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9390\/revisions\/9392"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9391"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9390"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9390"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9390"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}