{"id":9377,"date":"2026-04-28T08:30:48","date_gmt":"2026-04-28T08:30:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9377"},"modified":"2026-04-28T08:30:48","modified_gmt":"2026-04-28T08:30:48","slug":"gwamnan-jihar-neja-ya-ba-da-umarnin-gyaran-gaggawa-a-sansanin-nysc-da-ke-paiko","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-jihar-neja-ya-ba-da-umarnin-gyaran-gaggawa-a-sansanin-nysc-da-ke-paiko\/","title":{"rendered":"Gwamnan Jihar Neja Ya Ba Da Umarnin Gyaran Gaggawa A Sansanin NYSC Da Ke Paiko"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya hada kai da Ma\u2019aikatun Ayyuka, Matasa da Ci gaban Al\u2019umma domin tabbatar da gyaran gaggawa na rufin gine-ginen da iska ya kware da kuma wasu gine-gine da suka lalace a sansanin masu yi wa kasa hidima na National Youth Service Corps da ke Paiko.<\/p>\n<p>Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar ga manema labarai a Minna, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da damuwa.<\/p>\n<p>Tuni dai tawagar tantance barnar, wadda ta hada da Kwamishinar Ilimi, Dakta Hadiza Asabe Mohammed, Kwamishinan Matasa da Ci gaban Al\u2019umma, Jacob Baba Yisa, Darakta Janar na National Youth Service Corps, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, da kuma kodinetan NYSC na jihar, Misis Martina Shuaibu-Ibrahim, suka ziyarci wurin domin duba irin barnar da aka yi.<\/p>\n<p>Gine-ginen da abin ya shafa sun hada da dakunan kwanan maza masu yi wa kasa hidima, babban dakin taro na ayyuka daban-daban, kicin, gidajen ma\u2019aikata da kuma wasu sassan gidan kodinetan jihar.<\/p>\n<p>Gwamna Umar Bago ya bayyana cewa babu shakka wannan lamari ya jefa masu yi wa kasa hidima da jami\u2019an sansanin cikin wani hali na rashin jin dadi, yana mai cewa gyaran gaggawar da za a yi wa wuraren da suka lalace zai taimaka wajen bai wa matasan damar ci gaba da gudanar da atisayen tantancewa cikin kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Haka kuma, ya yaba wa tawagar tantancewar da kuma shugaban makarantar sakandaren Abubakar Dada Secondary School da ke Paiko bisa hadin gwiwar da suka yi na samar da azuzuwa a matsayin matsuguni na wucin gadi ga matasan da lamarin ya shafa.<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma sake tabbatar wa da NYSC cewa gwamnatinsa a shirye take domin tabbatar da tsaro da walwalar dukkan masu yi wa kasa hidima a fadin jihar.<\/p>\n<p>Aliyu Lawal\/Minna<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya hada kai da Ma\u2019aikatun Ayyuka, Matasa da Ci gaban Al\u2019umma domin tabbatar da gyaran gaggawa na rufin gine-ginen da iska ya kware da kuma wasu gine-gine da suka lalace a sansanin masu yi wa kasa hidima na National Youth Service Corps da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9378,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,6],"tags":[178],"class_list":["post-9377","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-nishadi","tag-nysc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/3170cf1f-689a-4e9d-bcdf-088d9932be23.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9377","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9377"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9377\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9379,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9377\/revisions\/9379"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9378"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9377"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9377"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9377"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}