{"id":9375,"date":"2026-04-28T08:28:26","date_gmt":"2026-04-28T08:28:26","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9375"},"modified":"2026-04-28T08:28:26","modified_gmt":"2026-04-28T08:28:26","slug":"yan-sandan-kwara-sun-kama-wadanda-ake-zargi-da-fashi-da-makami-da-kuma-kungiyoyin-asiri","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-sandan-kwara-sun-kama-wadanda-ake-zargi-da-fashi-da-makami-da-kuma-kungiyoyin-asiri\/","title":{"rendered":"&#8216;Yan Sandan Kwara Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashi Da Makami Da Kuma Kungiyoyin Asiri"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019yan sandan Jihar Kwara ta kama wasu da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma kasancewa mambobin kungiyar asiri da ke addabar yankin Amoyo a Ilorin.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa, jami\u2019ar hulda da jama\u2019a ta rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce kamen wani babban ci gaba ne a kokarin da rundunar ke yi na yaki da miyagun laifuka.<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa bayan samun rahoto a ofishin \u2019yan sanda na Amoyo kan wani hari da aka kai a mahadar Kabba Kajola, jami\u2019an tsaro suka gudanar da bincike cikin gaggawa wanda ya kai ga cafke Abdulazeez Isiaq, wanda aka fi sani da Pumpin, da kuma Rilwan Mohammed, yayin da ake ci gaba da neman wani da ake zargi wanda har yanzu bai shiga hannu ba.<\/p>\n<p>Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun kai hari ga wasu mutane, inda suka tilasta musu shiga wani ginin da ba a kammala ba wanda suke amfani da shi a matsayin maboya, sannan suka yi musu barazanar kisa tare da kwace musu kayayyakinsu masu daraja.<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara da cewa an samu kwato wata bindiga kirar gida da kuma daya daga cikin wayoyin da aka kwace daga hannun wadanda ake zargin, inda kuma suka amsa laifin da ake zarginsu da shi.<\/p>\n<p>Rundunar ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.<\/p>\n<p>Aliyu Muhammad Rabi\u2019u\/Kwara<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019yan sandan Jihar Kwara ta kama wasu da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma kasancewa mambobin kungiyar asiri da ke addabar yankin Amoyo a Ilorin. A cikin wata sanarwa, jami\u2019ar hulda da jama\u2019a ta rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce kamen wani babban ci gaba ne a kokarin da rundunar ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8738,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[175],"class_list":["post-9375","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kwara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/images.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9375","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9375"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9375\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9376,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9375\/revisions\/9376"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8738"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9375"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9375"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9375"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}