{"id":9371,"date":"2026-04-28T08:21:30","date_gmt":"2026-04-28T08:21:30","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9371"},"modified":"2026-04-28T08:26:51","modified_gmt":"2026-04-28T08:26:51","slug":"adc-kebbi-ta-nemi-a-mutunta-doka-da-adalci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/adc-kebbi-ta-nemi-a-mutunta-doka-da-adalci\/","title":{"rendered":"ADC Kebbi Ta Koka Kan Tsare Mambobinta"},"content":{"rendered":"<p>Jam\u2019iyyar ADC reshen Jihar Kebbi ta bayyana damuwa kan abin da ta kira kamawa da tsare mambobinta ba bisa ka\u2019ida ba a sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n<p>Sakataren jam\u2019iyyar a jihar, Abubakar Bawa Kalgo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam\u2019iyyar da ke Birnin Kebbi.<\/p>\n<p>Kalgo ya zargi wasu jami\u2019an gwamnatin Jihar Kebbi da amfani da bangaren shari\u2019a da wasu hukumomin gwamnati wajen tauye dimokuradiyya da kuma danniya ga jam\u2019iyyun adawa, inda ya yi kira ga hukumar kula da shari\u2019a ta kasa National Judicial Council da Hukumar Kula da Ma\u2019aikatan Shari\u2019a ta Jihar Kebbi da su shiga lamarin.<\/p>\n<p>Ya ce jam\u2019iyyar ADC a Kebbi na kira ga gwamnatin jihar da bangaren shari\u2019a da su mutunta doka, adalci da kuma ka\u2019idojin dimokuradiyya.<\/p>\n<p>A cewarsa, shugaban jam\u2019iyyar na jihar, Injiniya Sufiyanu Bala, wanda ya samu nasara bayan gudanar da zabukan cikin gida, jami\u2019an \u2018Yansanda sun kama shi bisa sammacin da Kotun Majistare ta Farko da ke Birnin Kebbi ta bayar.<\/p>\n<p>Kalgo ya kara da cewa an yi yunkurin gurfanar da shi a gaban wannan kotu sau da dama, amma abin bai yiwu ba saboda wasu kura-kurai na tsari da doka.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa duk da haka, \u2019yan sanda sun ci gaba da shirin gurfanar da shi bisa nacewar kotun, inda lauyan wanda ake zargin, Barrista A.A. Fingilla, ya bukaci alkalin kotun ya janye kansa daga shari\u2019ar bisa zargin son rai, amma kotun ta yi watsi da bukatar, lamarin da ya sa lauyan ya fice daga kotun.<\/p>\n<p>Sakataren jam\u2019iyyar ya kuma bayar da misalan wasu mambobi da aka kama tare da tsare su, ciki har da Umar Abubakar wanda aka fi sani da Abu Yarima, wanda ya shafe kwanaki 25 a tsare bisa zargin yin kalaman siyasa a kafafen sada zumunta, da kuma Husaina Ahmed Jega, Nasiru Garba Hashim da Umar Yakubu Kamba da sauransu.<\/p>\n<p>A cewarsa, jam\u2019iyyar ta yanke shawarar gabatar da koke ga National Judicial Council, Hukumar Kula da Ma\u2019aikatan Shari\u2019a ta Kebbi, Kungiyar Kare Hakkin Bil\u2019adama ta duniya wato Amnesty International, da kuma Ma\u2019aikatar Shari\u2019a ta Amurka domin neman a tsoma baki tare da kare dimokuradiyyar Nijeriya daga abin da ya kira amfani da hukumomin gwamnati wajen cimma muradun siyasa.<\/p>\n<p>Sai dai da yake mayar da martani, rundunar \u2018yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta musanta zargin tsare Injiniya Sufiyanu Bala ba bisa ka\u2019ida ba.<\/p>\n<p>Jami\u2019in hulda da jama\u2019a na rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa ana tsare da Sufiyanu Bala ne bisa sahihin umarnin kotu daga Kotun Majistare ta Birnin Kebbi, wanda ya umurci a tsare shi har zuwa ranar Litinin 27 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da shari\u2019a.<\/p>\n<p>Sanarwar ta jaddada cewa tsarewar tasa ya biyo bayan umarnin kotu ne, ba wai kama shi barkatai ba daga rundunar \u2019yan sanda.<\/p>\n<p>Rundunar ta kuma tabbatar da cewa a ranar da aka tsare shi, Injiniya Sufiyanu Bala ya bukaci kulawar lafiya, kuma nan take aka kai shi wani asibiti a Birnin Kebbi inda ake kula da lafiyarsa yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Dutsinma\/Kebbi<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jam\u2019iyyar ADC reshen Jihar Kebbi ta bayyana damuwa kan abin da ta kira kamawa da tsare mambobinta ba bisa ka\u2019ida ba a sassa daban-daban na jihar. Sakataren jam\u2019iyyar a jihar, Abubakar Bawa Kalgo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam\u2019iyyar da ke Birnin Kebbi. Kalgo ya zargi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9372,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1323],"class_list":["post-9371","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-adc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/e491b2be-b3ef-4057-9c26-fa58cb5d3aee.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9371","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9371"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9371\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9374,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9371\/revisions\/9374"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9372"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9371"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9371"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9371"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}