{"id":9368,"date":"2026-04-28T08:19:23","date_gmt":"2026-04-28T08:19:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9368"},"modified":"2026-04-28T08:19:23","modified_gmt":"2026-04-28T08:19:23","slug":"tsohon-shugaban-nphcda-ya-janye-daga-takarar-gwamnan-apc-ya-mara-wa-wadada-baya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tsohon-shugaban-nphcda-ya-janye-daga-takarar-gwamnan-apc-ya-mara-wa-wadada-baya\/","title":{"rendered":"Tsohon Shugaban NPHCDA Ya Janye Daga Takarar Gwamnan APC, Ya Mara Wa Wadada Baya"},"content":{"rendered":"<p>Tsohon Babban Daraktan Hukumar Bun\u0199asa Kula da Lafiya a Matakin Farko ta \u0198asa, Dr. Faisal Shu&#8217;aib, ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin jam\u2019iyyar APC.<\/p>\n<p>Dr. Faisal Shu\u2019aib ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, inda ya ce ya yanke shawarar janyewa daga takarar ne bisa yarjejeniyar da masu neman takarar suka yi cewa duk wanda aka zaba daga cikinsu, sauran za su mara masa baya domin tabbatar da nasarar jam\u2019iyyar mai mulki.<\/p>\n<p>Ya kuma sanar da hade tsarin yakin neman zabensa da na Sanata Ahmed Aliyu Wadada domin mara masa baya.<\/p>\n<p>A cewarsa, daga yau ya janye daga takarar gwamna, kuma zai ci gaba da goyon bayan Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda ya fi dacewa ya gaji Gwamna Abdullahi Sule a zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Dr. Faisal Shu\u2019aib ya ce a matsayinsu na Musulmi sun yi imani cewa mulki daga Allah yake zuwa, yana bayar da shi ga wanda Ya so a lokacin da Ya so, kuma yanzu lokaci ne na Sanata Ahmed Aliyu Wadada.<\/p>\n<p>Tsohon shugaban na National Primary Health Care Development Agency ya kuma yaba wa Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Abdullahi Sule bisa irin salon shugabanci mai kyau da suke aiwatarwa.<\/p>\n<p>Haka kuma ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya domin tabbatar da nasarar jam\u2019iyyar APC tun daga matakin mazaba har zuwa na \u0199asa baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Aliyu Muraki\/Lafiya<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tsohon Babban Daraktan Hukumar Bun\u0199asa Kula da Lafiya a Matakin Farko ta \u0198asa, Dr. Faisal Shu&#8217;aib, ya sanar da janyewarsa daga takarar gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin jam\u2019iyyar APC. Dr. Faisal Shu\u2019aib ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, inda ya ce ya yanke shawarar janyewa daga takarar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9369,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2049],"class_list":["post-9368","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-wadada"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/5c93101b-6697-40fd-8e71-8289b2b1f46d.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9368","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9368"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9368\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9370,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9368\/revisions\/9370"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9369"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9368"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9368"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9368"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}