{"id":9362,"date":"2026-04-27T08:14:20","date_gmt":"2026-04-27T08:14:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9362"},"modified":"2026-04-27T08:14:20","modified_gmt":"2026-04-27T08:14:20","slug":"2027-zan-dora-kan-kyawawan-ayyukan-marigayi-sanata-godiya-akwashiki-silas-agara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/2027-zan-dora-kan-kyawawan-ayyukan-marigayi-sanata-godiya-akwashiki-silas-agara\/","title":{"rendered":"2027: Zan Dora Kan Kyawawan Ayyukan Marigayi Sanata Godiya Akwashiki \u2013 Silas Agara"},"content":{"rendered":"<p>Tsohon Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta \u0198asa, National Directorate of Employment, Silas Ali Agara, ya \u0199addamar da kwamitin ya\u0199in neman za\u0253ensa domin neman kujerar Sanatan Nasarawa Ta Arewa gabanin babban za\u0253en shekarar 2027.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Akwanga, tsohon mataimakin gwamnan ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne bisa kiraye-kirayen da jama\u2019a da masu ruwa da tsaki suka yi masa domin ya ba da tasa gudunmawar wajen ci gaban yankin.<\/p>\n<p>Agara ya bayyana cewa yana da cikakken shiri da \u0199warewar shiga za\u0253en fidda gwani da kuma babban za\u0253e, idan har al\u2019ummar yankin suka ba shi goyon baya domin ya wakilce su a majalisar dattawa.<\/p>\n<p>Ya yabawa marigayi Godiya Akwashiki, wanda ya wakilci yankin a majalisar dattawa, yana mai cewa ya gudanar da ayyuka masu yawa kafin rasuwarsa, musamman wajen samar da ababen more rayuwa, \u0199arfafa matasa da mata, ilimi da koyar da sana\u2019o\u2019i.<\/p>\n<p>Silas Agara ya yi al\u0199awarin \u0257ora kan kyawawan ayyukan da marigayin ya fara tare da \u0199addamar da sababbin shirye-shirye domin jama\u2019a su ci moriyar dimokura\u0257iyya da ingantacciyar shugabanci.<\/p>\n<p>Ya ce ikon mulki daga Allah yake, kuma yana neman amincewar jama\u2019a domin ya wakilce su yadda ya kamata, tare da gode musu kan \u0199auna da goyon bayan da suke nuna masa.<\/p>\n<p>A cewarsa, daga cikin maza\u0253u 35 na yankin sanatocin Nasarawa ta Arewa, sun za\u0253i mutum 266 a matsayin tubalin ya\u0199in neman za\u0253ensu, wa\u0257anda ya ce an za\u0253e su ne bisa nagarta da \u0199warewar siyasa.<\/p>\n<p>Agara ya kuma yi al\u0199awarin tafiya da kowa tare da tabbatar da cewa ba zai yi watsi da al\u2019umma ba idan ya samu nasara.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Darakta Janar na kwamitin ya\u0199in neman za\u0253en, Mohammad Usman Aya, ya bu\u0199aci ha\u0257in kai da jajircewa daga masu ruwa da tsaki domin cimma burinsu.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bu\u0199aci al\u2019ummar jihar Nasarawa da su tabbatar sun kar\u0253i katin za\u0253e domin za\u0253ar shugabanni nagari da za su kawo ci gaba ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>Aliyu Muraki\/Lafiya<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tsohon Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyukan Yi ta \u0198asa, National Directorate of Employment, Silas Ali Agara, ya \u0199addamar da kwamitin ya\u0199in neman za\u0253ensa domin neman kujerar Sanatan Nasarawa Ta Arewa gabanin babban za\u0253en shekarar 2027. Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Akwanga, tsohon mataimakin gwamnan ya ce ya yanke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9363,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1038],"class_list":["post-9362","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-nasara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/22eba2ec-8e9b-4128-8340-eaaa9cac8a61.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9362","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9362"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9362\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9364,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9362\/revisions\/9364"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9363"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9362"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9362"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9362"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}