{"id":9353,"date":"2026-04-27T08:09:12","date_gmt":"2026-04-27T08:09:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9353"},"modified":"2026-04-27T08:09:12","modified_gmt":"2026-04-27T08:09:12","slug":"gwamnatin-tarayya-na-shirin-kaddamar-da-sababbin-shirye-shiryen-rage-talauci-a-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-na-shirin-kaddamar-da-sababbin-shirye-shiryen-rage-talauci-a-najeriya\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Na Shirin Kaddamar Da Sababbin Shirye-Shiryen Rage Talauci A Najeriya"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bayyana aniyarta na \u0199addamar da wani sabon shiri na kyauta da zai taimaka wajen fitar da \u2018yan \u0199asa daga talauci cikin tsari mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Ministan Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Dr Bernard Doro, ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma wa\u0257anda suka ci gajiyar shirin tallafin ku\u0257i na <strong>HOPE-CT<\/strong>, wanda aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.<\/p>\n<p>Ya ce manufar shirin ita ce tantance yadda tallafin gwamnati ke kawo sauyi a rayuwar gidaje marasa galihu. A cewarsa, a \u0199ar\u0199ashin shirin HOPE-CT, jihar Kwara ta samu kusan naira miliyan 13.7, yana mai bayyana jihar a matsayin abar koyi wajen aiwatar da shirin.<\/p>\n<p>Ministan ya yaba da yadda shirin ya kai ga al\u2019umma a matakai daban-daban, tare da jinjinawa gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq kan jagoranci da kulawar da yake bai wa walwalar jama\u2019a.<\/p>\n<p>A nata jawabin, Kwamishiniyar Jin-\u0199ai da Ci Gaban Jama\u2019a ta jihar, Dr Mariam Nnafatima Imam, ta ce shirin ya zo a kan lokaci kuma ya yi tasiri matu\u0199a.<\/p>\n<p>Ta bayyana cewa sama da gidaje dubu 183 ne suka amfana da tallafin a matakai uku na farko a dukkan \u0199ananan hukumomi 16 na jihar.<\/p>\n<p>Ta \u0199ara da cewa shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin jihar wajen tallafa wa marayu da yara marasa galihu da masu nakasa da tsofaffi da sauran marasa \u0199arfi, tare da inganta cibiyoyin kula da yara.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin wa\u0257anda suka ci gajiyar tallafin naira dubu 75,000, sun ce sun saka ku\u0257in ne cikin sana\u2019o\u2019in sayar da <strong>POP<\/strong> da gawayi, tare da gode wa gwamnatin tarayya bisa tallafin da ta bayar.<\/p>\n<p>Sun kuma ro\u0199i gwamnati da ta fa\u0257a\u0257a shirin domin \u0199arin mutane su samu damar cin gajiyarsa.<\/p>\n<p>Muhammad Rabiu\/Kwara<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bayyana aniyarta na \u0199addamar da wani sabon shiri na kyauta da zai taimaka wajen fitar da \u2018yan \u0199asa daga talauci cikin tsari mai \u0257orewa. Ministan Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Dr Bernard Doro, ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma wa\u0257anda suka ci [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9354,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2046],"class_list":["post-9353","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-pop"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/WhatsApp-Image-2026-04-24-at-9.55.30-PM.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9353","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9353"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9353\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9355,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9353\/revisions\/9355"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9354"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9353"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9353"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9353"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}