{"id":9350,"date":"2026-04-27T08:07:46","date_gmt":"2026-04-27T08:07:46","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9350"},"modified":"2026-04-27T08:07:46","modified_gmt":"2026-04-27T08:07:46","slug":"jamiyyar-adc-a-katsina-ta-za%c9%93i-sabbin-shugabanni","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamiyyar-adc-a-katsina-ta-za%c9%93i-sabbin-shugabanni\/","title":{"rendered":"Jam\u2019iyyar ADC A Katsina Ta Za\u0253i Sabbin Shugabanni"},"content":{"rendered":"<p>Jam\u2019iyyar ADC reshen jihar Katsina ta za\u0253i sabbin shugabanninta, inda aka za\u0253i Alhaji Mohammed Rimi a matsayin shugaban jam\u2019iyyar na jihar, sai Mansur Mu\u2019azu a matsayin mataimaki, Mukhtar Adahama a matsayin sakatare, yayin da Amina Lawal ta zama shugabar mata.<\/p>\n<p>An za\u0253i shugabannin ne yayin taron babban za\u0253en shugabannin jam\u2019iyyar na jihar, wanda ya ha\u0257a masu ruwa da tsaki da wakilai daga maza\u0253u 361 da shugabannin jam\u2019iyya daga matakan jiha da \u0199ananan hukumomi, tare da wakilai daga hedikwatar jam\u2019iyyar ta \u0199asa.<\/p>\n<p>A yayin rantsar da sabbin shugabannin, jigo a jam\u2019iyyar, Mustapha Inuwa, ya garga\u0257i mambobin jam\u2019iyyar da su yi taka-tsantsan da masu neman haddasa rikici a cikin jam\u2019iyyar gabanin za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci mambobin jam\u2019iyyar da su kasance masu ha\u0199uri da biyayya tare da mayar da hankali wajen \u0199arfafa tubalin jam\u2019iyyar, yana mai cewa al\u2019umma na \u0199ara nuna goyon baya ga jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bu\u0199aci hukumar zabe ta kasa da \u0253angaren shari\u2019a su tsaya tsayin daka wajen kare \u2018yancin kai da tabbatar da bin doka domin dorewar dimokura\u0257iyya.<\/p>\n<p>Wakilin hedikwatar jam\u2019iyyar ta \u0199asa, Lawal Batagarawa, ya yaba da yadda aka gudanar da za\u0253en cikin adalci, sannan ya ro\u0199i mambobi da su fifita muradun jam\u2019iyya fiye da na kansu domin samun ha\u0257in kai.<\/p>\n<p>Tun da farko, shugaban kwamitin za\u0253e, Babangida Talau, ya bayyana cewa an yi amfani da tsarin sasanci wajen za\u0253en shugabannin, kamar yadda dokokin za\u0253e suka tanada, tare da raba mu\u0199amai bisa daidaito tsakanin yankunan sanatoci uku na jihar.<\/p>\n<p>Sauran jiga-jigan jam\u2019iyyar sun bu\u0199aci sabbin shugabannin da su sake farfa\u0257o da jam\u2019iyyar tare da \u0199arfafa ta a matakin \u0199asa domin samun nasara a za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Isma\u2019ila Adamu\/Katsina<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jam\u2019iyyar ADC reshen jihar Katsina ta za\u0253i sabbin shugabanninta, inda aka za\u0253i Alhaji Mohammed Rimi a matsayin shugaban jam\u2019iyyar na jihar, sai Mansur Mu\u2019azu a matsayin mataimaki, Mukhtar Adahama a matsayin sakatare, yayin da Amina Lawal ta zama shugabar mata. An za\u0253i shugabannin ne yayin taron babban za\u0253en shugabannin jam\u2019iyyar na jihar, wanda ya ha\u0257a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9351,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[145],"class_list":["post-9350","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/dcc93773-4f94-4233-8f78-7fd215312b95.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9350","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9350"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9350\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9352,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9350\/revisions\/9352"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9351"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9350"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9350"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9350"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}