{"id":9341,"date":"2026-04-26T18:39:05","date_gmt":"2026-04-26T18:39:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9341"},"modified":"2026-04-26T18:39:05","modified_gmt":"2026-04-26T18:39:05","slug":"kauru-apc-ta-karfafa-hadin-kai-tare-da-tabbatar-da-goyon-bayan-tinubu-da-uba-sani","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kauru-apc-ta-karfafa-hadin-kai-tare-da-tabbatar-da-goyon-bayan-tinubu-da-uba-sani\/","title":{"rendered":"Kauru: APC Ta Karfafa Hadin Kai Tare da Tabbatar da Goyon Bayan Tinubu da Uba Sani"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu Kauru<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Masu ruwa da tsaki na jam\u2019iyyar APC a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna sun sake jaddada goyon bayansu ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani gabanin zaben shekarar 2027.<\/p>\n<p>Masu ruwa da tsakin, tare da hadin gwiwar shugabannin jam\u2019iyya a yankin, sun ce sabon hadin gwiwar da aka kulla na da nufin karfafa tattara magoya baya tun daga matakin karkara, da kuma tabbatar da nasarar APC a zaben.<\/p>\n<p>Sun kuma goyi bayan tsarin rabon mukaman siyasa bisa a yankuna uku na Karamar Hukumar Kauru, wato Masarautar Kumana, Masarautar Chawai da Masarautar Kauru. Inda suka jaddada muhimmancin adalci, gaskiya da daidaiton wakilci.<\/p>\n<p>A cewarsu, wannan tsarin rabon mukamai an tsara shi ne domin tabbatar da hada kai da kuma karfafa zumunci tsakanin al\u2019ummomin da ke karamar hukumar.<\/p>\n<p>Sanarwar da Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Bashir Tanko Dawaki ya fitar ta hannun Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Jama\u2019a, Yahaya Sa\u2019ad (Danruwatan Kauru), ta bayyana cewa masu ruwa da tsakin na da cikakken goyon baya ga gwamnatin Gwamna Uba Sani tare da kudurin inganta shugabanci nagari a fadin jihar.<\/p>\n<p>Har ila yau, masu ruwa da tsakin sun bukaci a kara bai wa mata da matasa dama a harkokin jagoranci da yanke shawara. Sun ce wannan kokari ya yi daidai da salon shugabancin Gwamna Uba Sani na bai wa kowa dama da tabbatar da adalci.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar masu neman takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna daga Masarautar Chawai, da kuma mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai daga Masarautar Kauru.<\/p>\n<p>Mahalarta taron sun bayyana wannan zama a matsayin alamar hadin kai da kuma jajircewa wajen ganin APC ta samu nasara a zaben 2027. Sun sake jaddada kudurinsu na goyon bayan gwamnatin Gwamna Uba Sani da kuma inganta shugabanci nagari a jihar.<\/p>\n<p>Masu ruwa da tsakin sun nuna kwarin gwiwa cewa hadin kai tsakanin Masarautar Kumana, Masarautar Chawai da Masarautar Kauru zai tabbatar da nasarar \u2018yan takarar APC a zaben mai zuwa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu Kauru Masu ruwa da tsaki na jam\u2019iyyar APC a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna sun sake jaddada goyon bayansu ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani gabanin zaben shekarar 2027. Masu ruwa da tsakin, tare da hadin gwiwar shugabannin jam\u2019iyya a yankin, sun ce sabon hadin gwiwar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9342,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[1205,33,1424],"class_list":["post-9341","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-apc","tag-kaduna","tag-kauru"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/IMG-20260426-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9341","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9341"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9341\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9343,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9341\/revisions\/9343"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9342"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9341"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9341"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9341"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}