{"id":9320,"date":"2026-04-22T16:13:18","date_gmt":"2026-04-22T16:13:18","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9320"},"modified":"2026-04-22T16:13:18","modified_gmt":"2026-04-22T16:13:18","slug":"majalisar-dokokin-jihar-kano-za-ta-tantance-murtala-sule-garo-a-matsayin-mataimakin-gwamna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-dokokin-jihar-kano-za-ta-tantance-murtala-sule-garo-a-matsayin-mataimakin-gwamna\/","title":{"rendered":"Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Tantance Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamna"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 12 domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna.<\/p>\n<p>Hakan ya biyo bayan karanta wasi\u0199a daga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya bu\u0199aci majalisar ta tantance tare da amincewa da nadin.<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore ne ya karanta wasikar yayin zaman majalisar.<\/p>\n<p>Ya ce gwamnan na neman amincewar majalisa ne domin nada Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna bisa tanadin Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.<\/p>\n<p>Bu\u0199atar ta biyo bayan murabus na son rai da tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi a ranar 27 ga watan Maris, 2026, wanda ya haifar da gurbi a kujerar.<\/p>\n<p>A cikin wasi\u0199ar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa nadin Garo ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da aka yi da shugabannin siyasa, da na addini da shugabannin al\u2019umma a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana wanda aka nada a matsayin gogaggen jami\u2019in gwamnati mai \u0199warewa, tare da gogewa a matakin \u0199asa da na jiha.<\/p>\n<p>Garo ya ta\u0253a rike mukamai da suka ha\u0257a da Mai Baiwa Gwamna Shawara kan harkokin jam\u2019iyyun siyasa, Shugaban \u0198aramar Hukumar Kabo, Shugaban \u0198ungiyar Shugabannin \u0198ananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Kano, da kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta.<\/p>\n<p>Gwamnan ya nuna \u0199warin gwiwa cewa gogewa, biyayya da fahimtar yanayin siyasa da gudanarwa da Garo ke da su za su taimaka wajen inganta shugabanci da samar da ribar dimokura\u0257iyya a jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma bu\u0199aci majalisar ta gaggauta duba wannan nadi tare da ba da amincewar da doka ta tanada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan tattaunawa, majalisar ta kafa kwamitin mutum 12 na tantancewar wanda Mataimakin Shugaban Majalisa, Muhammad Bello Butu Butu, ke jagoranta.<\/p>\n<p>Sauran mambobin kwamitin sun ha\u0257a da Shugaban Masu Rin\u0199aye, Babban Mai Tsawatarwa, Mataimakin Shugaban Masu Rin\u0199aye, Mai Tsawatarwa na Masu Rin\u0199aye, da \u2019yan majalisar da ke wakiltar Fagge, Sumaila, Warawa, Dawakin Kudu da Tudun Wada.<\/p>\n<p>Mataimakin Magatakarda na Majalisa ne zai kasance sakataren kwamitin.<\/p>\n<p>An ba kwamitin wa\u2019adin gabatar da rahotonsa ga majalisa ranar Litinin.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 12 domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna. Hakan ya biyo bayan karanta wasi\u0199a daga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda ya bu\u0199aci majalisar ta tantance tare da amincewa da nadin. Shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore ne ya karanta wasikar yayin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9322,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[39,211,2044,963],"class_list":["post-9320","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-kano","tag-majalisa","tag-mataimakin-gwamna","tag-nadi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/1728148298044-912x598-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9320","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9320"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9320\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9323,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9320\/revisions\/9323"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9322"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9320"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9320"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9320"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}