{"id":9233,"date":"2026-04-13T14:54:42","date_gmt":"2026-04-13T14:54:42","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9233"},"modified":"2026-04-13T14:54:42","modified_gmt":"2026-04-13T14:54:42","slug":"majalisar-jihar-kano-ta-bukaci-gwamnati-ta-kafa-cibiyoyin-ict","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-jihar-kano-ta-bukaci-gwamnati-ta-kafa-cibiyoyin-ict\/","title":{"rendered":"Majalisar Jihar Kano ta Bukaci Gwamnati ta Kafa Cibiyoyin ICT"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa cibiyoyin jarabawa da ake amfani da na&#8217;urar kwamfuta (CBT) a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, domin dacewa da sabon tsarin jarabawar kammala sakandare WAEC da NECO.<\/p>\n<p>An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa a zaman majalisar wanda Kakakin Majalisar, Jibril Falgore, ya jagoranta.<\/p>\n<p>Wannan kudiri ya fito ne daga dan majalisa mai wakiltar mazabar Madobi kuma Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar, Mukhtar Ishaq.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa sabon tsarin\u00a0 ya wajabta gudanar da jarabawa ta hanyar kwamfuta, yana mai jaddada bukatar gaggauta bai wa dalibai kwarewar amfani da na&#8217;urar ta kwamfuta.<\/p>\n<p>A cewarsa, kafa cibiyoyin kwamfuta (ICT) a fadin jihar zai taimaka wajen rage gibin fasahar zamani tare da shiryawa dalibai a birane da karkara domin fuskantar jarabawar ta CBT.<\/p>\n<p>Dan majalisa mai wakiltar mazabar Shanono\/Bagwai, Ali Lawan, ya goyi bayan kudirin, yana mai cewa lokaci ya yi kuma abu ne mai matukar muhimmanci.<\/p>\n<p>A wani labarin kuma, Majalisar ta bukaci gwamnatin jihar da ta kammala ayyukan samar da wutar lantarki a garuruwan Garun Madadi da Yarguruza da ke karamar hukumar Gwarzo.<\/p>\n<p>Wannan kudiri ya fito ne daga Yunusa Haruna, wanda ya jaddada cewa an riga an zuba kudade masu yawa a aikin, kuma kammala shi zai taimaka wajen magance matsalolin wutar lantarki da ake fama da su.<\/p>\n<p>Da yake goyon bayan kudirin, Sule Lawan Shuwaki mai wakiltar Tudun Wada ya ce kammala aikin zai bunkasa harkokin tattalin arziki a yankin.<\/p>\n<p>Haka kuma, Majalisar ta karbi rahoto kan kudaden Majalisar Masarautar Rano na shekarun 2023\u20132024, sannan ta amince da kudirori kan gyaran Dam din Buda a Garko da kuma gina hanya a Makoda.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta kafa cibiyoyin jarabawa da ake amfani da na&#8217;urar kwamfuta (CBT) a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, domin dacewa da sabon tsarin jarabawar kammala sakandare WAEC da NECO. An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa a zaman majalisar wanda Kakakin Majalisar, Jibril [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9234,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,1,11],"tags":[2034,2033,39,211],"class_list":["post-9233","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-cbt","tag-ict","tag-kano","tag-majalisa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/Screenshot_20241103-095511_1-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9233","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9233"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9233\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9235,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9233\/revisions\/9235"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9234"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9233"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9233"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9233"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}